Zamfara: An Damke Masu Samarwa ‘Yan Bindiga Layikan Waya da Maganin Karfin Maza

Zamfara: An Damke Masu Samarwa ‘Yan Bindiga Layikan Waya da Maganin Karfin Maza

  • Kwamitin yaki da ‘yan daba a jihar Zamfara sun tabbatar da damke wasu mutum uku da ake zargi da kai wa ‘yan bindiga layikan waya
  • Ana zargin su da samarwa ‘yan bindiga miyagun kwayoyi, maganin karin karfin maza, akuskura, maganin shake da sauransu
  • Har ila yau, kwamitin ya sanar da cewa sun cafke wasu matasa da suka kware wurin kwace wayar mutane har da ‘yan biki

Zamfara - Kwamitin yaki da dabanci na gwamnatin jihar Zamfara sun tabbatar da kama wasu mutum uku da ake zargi da samarwa ‘yan bindiga layikan waya, kwayoyi da maganin karfin maza.

Zamfara Map
Zamfara: An Damke Masu Samarwa ‘Yan Bindiga Layikan Waya da Maganin Karfin Maza. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

TheCable ta rahoto cewa, kwamitin ya kama wasu mutum uku kan zargin kwacen waya.

Bello Bakyasuwa, shugaban kwamitin yayi maganar a ranar Lahadi yayin mika wadanda ake zargi hannun jami’an tsaro a Gusau, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane

Gwamnatin jihar Zamfara a baya-bayan nan ta kafa kwamitin taimakawa jami’an tsaro a kokarin yaki da ‘yan daban siyasa da sauran masu laifuka a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Kun san bayan kafa kwamitin tare da wakilai daga hukumomin tsaro da Gwamna Bello Matawalle yayi, an kallafa mana nauyin yaki da ‘yan saba da sauran laifuka a kansu.”

- Yace.

“A ranar Asabar, yayin sintiri da tsakar dare mun kama wasu ababen hawa a kan titin Gusau zuwa Magami inda aka samu layikan waya 100, akuskura, abun shake, maganin karfin maza da kwayoyi.
“Kun san gwamnatin jihar ta hana kaiwa da kawowa cikin dare a yankin da ababen hawan.
“Daya daga cikin aikinmu shi ne tabbatar da an bai dokar gwamnati.”

- Ya kara da cewa.

Ya kara da cewa wasu mutum uku da ake zargin an kama su bayan sun kai hari kan wasu ‘yan biki a yankin Tudun Wada ta Gusau a yammacin Asabar.

Kara karanta wannan

An Yi Watsi Da Sunan Rarara a Kwamitin Kamfen Din Tinubu

“‘Yan daba a Gusau sun samu sabon hanyan sace wayoyi a bukukuwa.”

- Yace.

“Bayan samun rahoto kan lamarin a yankin Tudun Wada, mun kama wasu mutum uku da ake zargi tare da samun wayoyi a wurinsu.
“Sauran wadanda ake zargin sun tsere amma mutanenmu suna aiki tukuru don ganin an kama su.”

- Ya kara da cewa.

Sojoji Sun Ragargaza Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Zamfara, Chire

A wani labari na daban, Dakarun sojin Najeriya dake aiki da Rundunar Operation Hadarin Daji sun harbe daya daga cikin gagararren shugabannin ‘yan bindiga na Zamfara.

Daily Trust ta rahoto cewa, kwamandan an gano sunansa Ibrahim Chire wanda ke addabar yankunan Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka.

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami a wata takarda da ya fitar a daren Alhamis, yayi bayanin cewa an halaka ‘dan ta’addan ne bayan musayar wutan da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel