2023: Yan Daba Sun Farmaki Jirgin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna Na PDP

2023: Yan Daba Sun Farmaki Jirgin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna Na PDP

  • Tsagerun yan Daban siyasa sun kai wa ayarin kamfen mai neman zama gwamna Legas a inuwar jam'iyyar PDP
  • A wata sanarwa da PDP ta fitar, tace da yawan yan tawagar sun jikkata cikinsu har da manema labarai
  • Jam'iyyar ta bukaci kwamishinan yan sandan jihar Legas ya zakulo masu hannu a harin domin su girbi abinda suka shuka

Lagos - Wasu yan Daba sun farmaki jirgin yaƙin neman zaben Olajide Adediran, ɗan takarar gwamnan jihar Legas karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben 2023.

A wata sanarwa da shugaban PDP reshen Legas, Hakeem Amode, ya fitar, yace an farmaki Adediran wanda aka fi sani da Jandor a yankin Ikoga junction, ƙaramar hukumar Badagary ranar Lahadi.

Olajide Adediran.
2023: Yan Daba Sun Farmaki Jirgin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamna Na PDP Hoto: thecable
Asali: UGC

Amode ya bayyana cewa mutane da yawa dake cikin tawagar sun jikkata sakamakon harin cikinsu har da yan jarida, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Motocin Yakin Neman Zaben PDP Na Wata Jiha Sun Ta Da Kura, Babu Hoton Atiku Abubakar

"Yan Daban da APC ta ɗauki nauyi sun kai hari ga ayarin kamfen ɗan takarar gwamnan PDP a hanyar dawowa daga ziyarar mambobin jam'iyya a Ikoga junction, ƙaramar hukumar Badagary."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Harin ya yi sanadin raunata da yawan mambobin tawagar Jandor da manema labarai. A yanzu haka akawai ɗan jaridar da ke cikin mawuyacin hali a wani Asibiti yayin da aka yi wa sauran maganin raunukansu."
"Maharan da suka farmaki ayarin kamfen sun bude wuta suna kiran APC kana sun yi amfani za muggan makamai. Idan baku manta ba mun yi zargin APC na shirin amfani da yan daba don kai hari ga ɗan takararmu, Jandor."

- Hakeem Amode.

Wane mataki PDP zata ɗauka bayan harin?

Shugaban PDP na Jihar Legas ya yi kira ga hukumomin tsaro su gaggauta binciko masu hannu a harin tare da hukunta su domin kare faruwar haka nan gaba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

"Muna kira ga kwamishinan yan sandan Legas, kwamandan yan sandan yankin Badagary su yi duk me yuwuwa don kamo masu hannu a lamarin kana a hukunta su domin kare haka nan gaba."
"Haka nan muna gargaɗin duk wasu gurɓatattu dake kulla-kullar ta da yamutsi a wurin kamfe da zaɓe mai zuwa cewa ba zamu zuba ido muna kallonsu ba, zamu ɗauki duk kalar wulaƙancin da suka ɓullo da shi."

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a ranar Asabar Jandor yace Allah ya zabi PDP ta lashe zabukan 2023 a jihar kuma shi da abokin takararsa sun zo ne domin ceto jihar ta amfani al'umma.

A wani labarin kuma PDP a Jihar Filato Ta Yi Wa Atiku Abubakar Alkawarin Kuri'u Miliyan Biyu a Zaben 2023

Jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta dauki alkawarin kawowa Atiku Abubakar kuri'u miliyan biyu gabannin 2023.

Babbar jam'iyyar adawar kasar ta kuma sha alwashin lashe dukkanin kujerun siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna da Wasu Sun Koma PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel