An Yi Kazamin Arangama Tsakanin Yan Tasha Da Yan Kasuwa, Ana Fargabar Rasa Rayyuka

An Yi Kazamin Arangama Tsakanin Yan Tasha Da Yan Kasuwa, Ana Fargabar Rasa Rayyuka

  • Ana Fargabar Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Yayin Da Yan Kasuwa Da Yan Daba Suka Yi Arangama A Kasuwar Alaba
  • Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 9 na safiyar ranar Laraba hakan ya tilasta wa mutane rufe shagunansu
  • Benjamin Hundeyin, kakakin yan sandan Jihar Legas ya ce an tura jami'an yan sanda da sojoji zuwa yankin don kwantar da tarzoma

Legas - Rikici ya barke a ranar Laraba tsakanin wasu da ake zargin yan daban tashar mota ne da wasu yan kasuwa a shahararren kasuwar Alaba da ke Ojo a Legas, rahoton Daily Trust.

A kalla wasu mutane biyu da ba a bayyana sunansa ba sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a rikicin da ya barke misalin karfe 9 na safe.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Rikici
An Yi Kazamin Arangama Tsakanin Yan Tasha Da Yan Kasuwa, Ana Fargabar Rasa Rayyuka. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan kasuwa da dama wadanda da farko sun bude shagunansu sun yi gaggawa sun rufe saboda tsoron kada rikicin ya ritsa da su.

Shaidun gani da ido sun ce yan daba da dama sun yi yunkurin shiga kasuwar su fi karfin jami'an tsaron kasuwar a ranar Talata amma ba su yi nasara ba.

Kowa ya watse a kasuwar da ta fara daga karamar hukumar Ojo a lokacin da wakilin Daily Trust ya ziyarci wurin.

Amma, an tura jami'an rundunar yan sandan Najeriya daga tawagar RRS da sojoji daga Ojo zuwa yankin.

Martanin Rundunar Yan Sanda

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya ce rikicin tsakanin wasu yan kasuwa ne da yan daban tasha.

Idan za a iya tuna wa a baya-bayan nan, gwamnatin jihar Legas ta haramta ayyukan manyan kungiyoyin sufuri biyu a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Wata Jiha a Najeriya Ya Rasu

'Yan Daba' Sun Kai Hari A Wurin Taron Kamfen Din Atiku A Kaduna

A wani rahoton, an yi hayaniya a filin wasanni na Ranchers Bees da ke Kaduna, wurin da aka yi taron dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, yayin da wasu da ake zargin yan daba ne suka kai wa magoya baya jam'iyyar hari.

Yan daban, wadanda suke dauke da muggan makamai kamar adduna da sanduna sun rika jefa da duwatsu ga mutanen da suka halarci taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel