Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Jiha a Najeriya Ya Rasu

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Jiha a Najeriya Ya Rasu

  • Al'ummar Ekiti za su yi kwanan bakin ciki yayin da kakin majalisar dokokin jihar, Funminiyi Afuye, ya kwanta dama
  • Hon Funminiyi Afuye mai wakiltan mazabar Ikere 1 ya rasu ne a yammacin yau Laraba bayan yar gajeruwar rashin lafiya
  • Marigayi ya halarci bikin rantsar da sabon gwamnan jihar ranar Lahadi sannan a jiya Talata ya halarci zaman majalisa

Ekiti - Kakakin majalisar dokokin jihar Ekiti, Hon Funminiyi Afuye ya rasu yana da shekaru 66 a duniya, jaridar The Nation ta rahoto.

Afuye wanda ke wakiltan mazabar Ikere 1 ya rasu ne a yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, bayan yar gajeruwar rashin lafiya.

Funminiyi Afuye
Da Dumi-dumi: Allah Ya Yiwa Kakakin Majalisar Ekiti Rasuwa Hoto: Lere Olayinka
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta rahoto cewa wani dan majalisa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce marigayin ya kamu da rashin lafiya inda aka kwashe shi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ekiti da ke Ado-Ekiti a safiyar yau Laraba.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Marigayin ya halarci bikin rantsar da sabon gwamnan jihar, Biodun Oyebanji, wanda aka yi a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma tattaro cewa marigayin ya halarci taron majalisar dokokin jihar a ranar Talata kafin faruwa labarin mara dadi a yau Laraba.

2023: Da Ace Ni Ba Dan PDP Bane, Da Zan Taimaki Peter Obi Ya Zama Shugaban Kasa, Gwamnan Arewa

A wani labari na daban, gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana cewa ba don shi dan PDP bane da babu abun da zai hana shi aiki don ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya lashe zabe mai zuwa.

Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, yayin da ya karbi bakuncin tsohon gwamnan na jihar Ana,bra a gidansa da ke Abuja, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jami'ar ABU Zaria Ta Sanar da Ranar Koma Wa Karatu Gada-Gadan Bayan Janye Yajin ASUU

Ya bayyana Obi, Bola Tinubu na APC, da Atiku Abubakar na PDP a matsayin manyan yan takara sannan ya bukaci yan Najeriya da su zabi wanda yafi cancanta a tsakaninsu ba tare da son zuciya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel