'Yan Daba' Sun Kai Hari A Wurin Taron Kamfen Din Atiku A Kaduna

'Yan Daba' Sun Kai Hari A Wurin Taron Kamfen Din Atiku A Kaduna

  • Yan daba da ake zargin hayansu aka dakko sun yi kai wa magoya bayan jam'iyyar PDP hari a wurin taron kamfen din Atiku a Kaduna
  • Wani daga cikin mutane da ya halarci taron kuma ya tsere ya ce maharan suna dauke da adduna, sanduna da wasu makamai kuma sun yi kwacen waya
  • Rundunar Yan sandan jihar Kaduna ta ce ta tura jami'anta sun kwantar da tarzoma kuma Atiku Abubakar ya yi tir da harin ya yi kira ga Shugaba Buhari ya ja kunnen jam'iyyun siyasa

Kaduna - An yi hayaniya a filin wasanni na Ranchers Bees da ke Kaduna, wurin da aka yi taron dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, yayin da wasu da ake zargin yan daba ne suka kai wa magoya baya jam'iyyar hari.

Kara karanta wannan

Tashin hakali: 'Yan kwangilar maganin yaki da Korona sun tsoho ma'aikata a Abuja, suna zanga-zanga

Yan daban, wadanda suke dauke da muggan makamai kamar adduna da sanduna sun rika jefa da duwatsu ga mutanen da suka halarci taron.

Yanzu
'Yan Daba' Sun Kai Hari A Wurin Taron Kamfen Din Atiku A Kaduna
Asali: Original

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wakilin Daily Trust da ke wurin ya ga mutane suna guje-guje don neman tsira.

An gano tattaro cewa yan daban sun kwace wayoyin salulan mutane da suka halarci taron.

Daya daga cikin wanda ya tsere daga wurin taron ya fada wa Daily Trust cewa:

"Sun kwace wayoyin mutane a kofa kafin shiga wurin taron. Zan koma gida domin ban taho nan don in mutu ba ko jin rauni domin Allah kadai ya san yan daban ko wanda ya aiko su."

Martanin Atiku kan harin

Da ya ke magana kan harin, Atiku ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi magoya bayan sauran jam'iyyun.

Kara karanta wannan

Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU

Ya ce:

"Yanzu na samu rahoton gaggawa kan harin da aka kai wa magoya bayan @OfficialPDPNig da yan daba da aka dauki haya suka kai a wurin taron kamfen din PDP a Jihar Kaduna. Wannan ya saba wa demokradiyya kuma ya saba da yarjejeniyar zaman lafiya da dukkan jam'iyyu suka ratabba hannu a kai makonni da suka wuce."

"Ina kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga dukkan jam'iyyu su ja kunnen magoya bayansu da mambobi don tabbatar da an yi kamfen da ma zabe cikin zaman lafiya da adalci."

Martanin yan sanda

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ce an tura jami'an tsaro wurin.

Ya ce:

"Jami'an mu sun fatattaki yan daban kuma yanzu hankulan mutane ya kwanta a wurin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel