Obajana: Duk da Gwamnatin Tarayya Ta Tsoma Baki, Gwamnatin Kogi Ta Kai Dangote Kotu

Obajana: Duk da Gwamnatin Tarayya Ta Tsoma Baki, Gwamnatin Kogi Ta Kai Dangote Kotu

  • Za ayi shari’a nan gaba a kotu tsakanin Gwamnatin jihar Kogi da kamfanin Dangote Industries Ltd
  • Dangote Industries Limited ne suke da kamfanin Dangote Cement Plc da aka samu sabani da su a jihar Kogi
  • Gwamnatin Kogi tana so kotu ta duna yarjejeniyar da aka shiga da Dangote tun a shekarun 2002 da 2003

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta shigar da kara a kan kamfanin Dangote Industries Limited wanda ya mallaki kamfanin siminti na Dangote Cement Plc.

This Day tace gwamnatin Kogi ta shigar da kara a dalilin sabanin da aka samu game da mallakar kamfanin siminti na Obajana da yake Oworo a jihar Kogi.

Kamar yadda takardar karar mai lamba HcL/8T/2022 ta nuna, za ayi a shari’a tsakanin Gwamnati da kamfanin a babban kotun jiha da ke Lokoja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

A ranar 18 ga watan Oktoban 2022, gwamnatin Kogi ta shigar da kara a gaban Alkali, tana mai neman a raba gardamar da ke tsakaninta da kamfanin.

An dauko maganar shekaru 20

An nemi kotu ta duba yarjejeniyar da aka yi takanin Gwamnatin Kogi da Dangote Industries Limited a karshen Yulin 2002 da kuma Fubrairun 2003.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin gwamnati sun ce ba a bi ka’ida wajen shiga yarjejeniya shekaru 20 da suka wuce ba.

Dangote
Kamfanin simintin Dangote Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Punch ta kara da cewa idan har hakan ta tabbata, gwamnatin Kogi ta roki Alkali ya soke yarjejeniyar da ke tsakanin bangarorin domin an rasa ginshiki.

Bugu da kari, gwamnatin jihar tana ikirarin kamfanin na Dangote ba zai iya cin moriyar wata dama, riba ko amfani daga yarjejeniyar nan da aka yi ba.

Har ila yau, gwamnatin Kogi tana so kotu ta takawa Dangote Industries Limited burki, ta hana kamfanin amfana da yarjejeniyar da aka sa wa hannu.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

Ba a sa ranar zama ba tukuna

Jaridar ta nemi jin ta bakin sashen rajistar kamfani da Dangote, amma ba ayi nasarar samun su ba. Har zuwa yanzu ba a sa lokacin da za a saurari shari’ar ba.

A cikin takardun da aka bada domin gamsar da kotu, akwai bayanin SSG, Folashade Arike Ayoade da tace jihar Kogi tayi wa kamfanin Obajana rajista a 1992.

Yadda muka mallaki Obajana - DIL

Kwanaki kun samu labari cewa wani jawabi da aka fitar ya yi karin haske a kan sabanin da ya shiga tsakanin Dangote da kuma gwamnatin jihar Kogi.

Shugabannin kamfanin Dangote Industries Ltd sun ce sun biya kudi wajen sayen kamfanin Obajana a 2002, kuma gwamnatin tarayya ta ba su lasisi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel