Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

  • Babbar kotun tarayya da ke zama a Damaturu ta soke zaben fidda gwani biyu APC ta gudanar na majalisar dokoki a jihar Yobe
  • Mai shari’a Justis Fadima Murtala Aminu, ta zartar da hukuncin ne a kan mazabun Fika/Ngalfa da Jaskusko
  • Ta kuma bayar da umurnin gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 14 yayin da ta gargadi jam'iyyar mai mulki kan kutse a sunayen wakilai

Yobe - Babbar kotun tarayya da ke zama a Damaturu ta soke zaben fidda gwani biyu da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gudanar na majalisar dokoki a jihar Yobe.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa mazabun da abun ya cika da su sune Fika/Ngalfa da Jaskusko.

A yanzu haka APC bata da yan takara a mazabun
Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa Hoto: Yobe State APC Social Media Forum
Asali: Facebook

Justis Fadima Murtala Aminu, wacce ta zartar da hukunci, ta umurci APC da ta gudanar da sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 14.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu Sabbin Hotuna Daga Aso Villa Sun Nuna Tinubu Na Kus-Kus da Mataimakin Buhari

Justis Fadima ta kuma gargadi jam’iyyar da kada ta yi kutse a jerin sunayen sahihan wakilai da aka aikewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangare daya, kotun ta kuma kori shari’ar Abubakar Jinjiri da Bashir Machina da APC.

Idan Atiku Ya Lashe Zaben 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay

A wani labarin, Shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara kan harkar barayi da rashin gaskiya, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fallasa kansa a matsayin wanda ke kyamar yan kudu.

Sagay wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa mutanen kudu zasu dandana kudarsu idan har Atiku ya kashe babban zaben 2023 mai zuwa, rahoton Daily Independent.

Atiku, a wajen wani taron da kwamitin hadin gwiwa na arewa ya shirya, ya bukaci mutanen arewa da kada su zabi dan takarar shugaban kasa Bayarabe ko Ibo a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

Asali: Legit.ng

Online view pixel