Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

Kamfen 2023: 'Yan A Mutun APC Na Bin Gida-gida Don Tallata Dan Takararsu Bola Tinubu A Wata Jahar Arewa

  • Gabannin zaben 2023, kungiyar magoya bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, sun kai kamfen dinsu zuwa mataki na gaba
  • Kungiyar Jagaban National Coalition ta fara bi gida-gida tana yiwa tsohon gwamnan na jihar Lagas kamfen a jihar Plateau
  • Jagoran kungiyar a Plateau, Mista Zakariyau Adigun, ya ce za su wayarwa gaba daya mutanen jihar kai kan nasarorin da Tinubu ya samu

Plateau - Wata kungiyar goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai suna Jagaban National Coalition ta fara bi gida-gida tana yi masa kamfen.

Jagoran kungiyar a jihar Plateau, Mista Zakariyau Adigun, ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a garin Jos, a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Zai Lashe Zabe a Arewa, Ya Dare Kujerar Shugaban Kasa a 2023, Dan Kashenin Buhari

Bola Tinubu
Kungiyar Goyon Bayan Tinubu Sun Fara Bi Gida-Gida Suna Masa Kamfen A Wata Jahar Arewa Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Adigun ya ce shirin kungiyar shine sanar da duk wani dan jihar nasarorin Tinubu da kyawawan shirin da yake yiwa kasar, rahoton Vanguard.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun kai kamfen dinmu har gida-gida muna tallata dan takararmu ga masu zabe.
“Tinubu ya gyara Lagas sannan ya kafa tsarin da babu wata jiha a kasar nan da za ta tsayawa da ita.
“Yana da karfin da zai iya mayar da Najeriya kasa mafi daukaka a nahiyar Afrika.
“Mun yarda cewa yana da karfin da zai iya magance matsalolin tattalin arzikin da kasar nan ke fama da su.”

Ya kuma bayyana cewa dan takarar shugaban kasar na APC zai magance matsalolin tsaro don ba yan Najeriya damar yin harkokinsu ba tare da tangarda ba.

A karshe ya jinjinawa shugaban APC a jihar Plateau, Cif Rumus Bature kan kokarin da yake yi don tabbatar da ganin cewa jam’iyyar tayi nasara a zaben 2023, rahoton PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari

Idan Atiku Ya Lashe Zaben 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay

A wani labari, shugaban kwamitin PACAC, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fallasa kansa a matsayin wanda ke kyamar yan kudu.

Sagay wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa mutanen kudu zasu dandana kudarsu idan har Atiku ya kashe babban zaben 2023 mai zuwa, rahoton Daily Independent.

Atiku, a wajen wani taron da kwamitin hadin gwiwa na arewa ya shirya, ya bukaci mutanen arewa da kada su zabi dan takarar shugaban kasa Bayarabe ko Ibo a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel