Yadda Muka Bi, Muka Mallaki Obajana shekaru 20 da suka wuce - Kamfanin Dangote

Yadda Muka Bi, Muka Mallaki Obajana shekaru 20 da suka wuce - Kamfanin Dangote

  • Wani jawabi da aka fitar ya yi karin haske a kan sabanin da ya shiga tsakanin Dangote da gwamnatin jihar Kogi
  • Shugabannin kamfanin Dangote Industries Limited sun ce sun biya kudi wajen sayen kamfanin Obajana a 2002
  • Dangote yace gwamnatin tarayya ta ba shi lasisin hako ma’adanai, kuma yana biyan jihar Kogi harajin da ya dace

Abuja - Shugabannin kamfanin Dangote Industries Limited sun bayyana cewa an bi dokoki wajen sayen filin kamfanin simintin Obajana a shekarar 2002.

This Day tace wannan bayani ya sabawa matsayar gwamnatin jihar Kogi, wanda take cewa an mallaki kamfanin ne ba tare da an bi ka’ida da doka ba.

Bugu da kari Dangote Industries Limited yace yana biyan gwamnatin Kogi haraji da duk wasu kudi da suka kamata tun lokacin da suka fara aiki a 2007.

Kara karanta wannan

Rikicin Mallaka: Dangote da Yahaya Bello Sun Gurfana a Fadar Buhari Za a Yi Musu Sasanci

A wani jawabi da kamfanin ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba 2022 ne ya yi wannan karin haske. The Nation ta kawo wannan labari a rahotanninta.

“A 2003, kamfanin Dangote Industries Limited ita kadai ta saye kasar da aka gina kamfanin simintin Obajana, bayan ta saye hannun jarin kamfanin a 2002.
An yi hakan ne bayan yarjejeniyar da ta shiga da KSG domin sa hannun jari a jihar Kogi. An ba DIL satifiket uku bayan biyan kudi, kuma aka sallami masu fili.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Dangote Industries Limited

Kamfanin Dangote
Shugaban DIL, Aliko Dangote Hoto: NMEP Nigeria
Asali: UGC

Hakan na zuwa ne bayan an samu sabani tsakanin kamfanin da gwamnatin Yahaya Bello.

Jawabin ya tabbatar da cewa DIL kadai ya biya kudi ya saye kamfanin, bayan nan ya saye hannun jari a kamfanin simintin Obajana shekaru 20 da suka wuce.

Kara karanta wannan

Kasafin Kudi: Buhari Ya Fadawa Majalisa Ba Zai Cigaba da Biyan Tallafin Fetur a 2023 ba

Jihar Kogi ba ta da iko da ma'adananta

Kamfanin yace a dokar Najeriya, gwamnatin tarayya take da iko da ma’adanan da ke karkashin kasar jihar Kogi, don haka ita ke bada lasisin hako ma’adanai.

Dangote Industries Limited yace gwamnatin jihar Kogi ba ta da ikon bada lasisin amfani da arzikin da ke karkashin kasanta domin ba huruminta ba ne.

Yarjejeniyar da Dangote ya shiga da gwamnatin Kogi tayi sanadiyyar da kamfanin ya jawo mutane suka samu ayyukan yi, kuma jihar ta rika samun haraji.

Gwamnatin Kogi na son karbe Obajana

An samu labari Gwamnatin Kogi tayi bincike a kan saida kamfanin simintin Obajana da aka yi a can baya, ana zargin an saba doka a mallakar kamfanin.

Binciken da SSG, Folashade Ayoade ta gudanar ya nuna ba Dangote Industries Limited suke da mallakar kamfanin ba, kuma ba a biyan jihar haraji.

Kara karanta wannan

Bakano ya girgiza intanet, ya kera keke napep din da ta ba 'yan Najeriya mamaki

Asali: Legit.ng

Online view pixel