Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Rufe Gidajen Talabijin da Rediyo Saboda Rashin Da'a

Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Rufe Gidajen Talabijin da Rediyo Saboda Rashin Da'a

  • Gwamnatin Zamfara karkashin Bello Matawalle ta rufe wasu gidajen talabijin guda uku da na radiyo daya saboda rashin da'a
  • Matawalle ya hana gudanar da duk wasu gangamin siyasa saboda rashin tsaro a jihar amma sai PDP tayi biris da haka ta yi wani taro
  • Gidajen labaran da abun ya shafa sun halarci gangamin na PDP don samo rahoto duk da sun san matsayin gwamnati kan haka

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe gidajen talabijin uku da gidan radiyo daya a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoba, saboda saba ka'idar aikinsu.

Gidajen talabijin da abun shafa sun hada da NTA, Gamji TV, Al-umma TV da Pride FM dukkansu a Gusau, babban birnin jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Mun Shriya Tsaf Don Yiwa Kwankwaso da Ganduje Ritayar Dole a Siyasa, ‘Dan Takarar Gwamna a LP

Matawalle
Zamfara: Gwamna Matawalle Ya Rufe Gidajen Talabijin da Rediyo Saboda Rashin Da'a Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A wani jawabin radiyo, kwamishinan labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya ce an rufe gidajen labaran ne saboda sun keta ka'idar aikinsu.

A cewar Dosara, gidajen labaran da abun ya shafa sun halarci gangamin da jam'iyyar adawa ta People's Democratic Party (PDP) ta shirya a jihar wanda tun farko gwamnatin jihar ta haramta shi saboda dalilai na tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Gwamnatin jihar ta dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar saboda matsalolin rashin tsaro Amma sai PDP tayi watsi da umurnin sannan ta gudanar da wani gangami a Gusau, babban birnin jihar inda aka kashe mutum daya da jikkata wasu 18.

Kara karanta wannan

Ba'a Rabu da Bukar Ba: Har Yanzu Akwai Barazanar Ambaliyar Ruwa A Nijeriya, NiMet

"Gidajen labarai hudu, NTA, Gamji TV, Al-umma TV da Pride FM suma sun halarci taron don daukar rahoto duk da cewar suba sane da haramta harkokin siyasa da gwamnatin jihar tayi.
"Duba ga wannan, an rufe gidajen watsa labaran nan take."

A halin da ake ciki, gwamnatin ta umurci jami'an tsaron gidajen labaran da suka yi kokarin keta umurnin ta hanyar shiga ofishoshinsu don yin kowani aiki, rahoton Premium Times.

Kotu Ta Haramtawa EFCC Kwace Wasu Manyan Kadarorin Gwamna Matawalle

A wani labarin, mun ji cewa kotu ta hana hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) kwace wasu kadarori shida da aka gano suna da alaka da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ce ta bayar da wannan umurnin a ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Mazaunin Gidan Haya Ya Sace Mai Gidan Tare da Karɓar Naira Miliyan 1

Da yake zartar da hukuncin, alkalin kotun, Justis Inyang Ekwo, ya yi amfani da sashi na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya baiwa gwamnoni kariya daga fuskantar shari’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel