Kotu Ta Haramtawa EFCC Kwace Wasu Manyan Kadarorin Gwamna Matawalle

Kotu Ta Haramtawa EFCC Kwace Wasu Manyan Kadarorin Gwamna Matawalle

  • Wata babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta hana kwace filaye shida na Gwamnan jihar Zamfara dake Abuja wanda EFCC ta zaburo a kan hakan
  • Alkalin ya Amin ta da matsayar lauyan Gwamna Matawalle na cewa kotu bata da wannan hurumin ganin cewa Matawalle Gwamna ne mai ci yanzu
  • Tun farko da kotun ta kwace filayen shida da suka suke Abuja na wucin-gadi amma yanzu ta mayarwa Gwamnan don biyayya ga kundin tsarin mulki

FCT, Abuja - Kotu ta hana hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) kwace wasu kadarori shida da aka gano suna da alaka da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ce ta bayar da wannan umurnin a ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Wike Ya Dauki Ortom, Makinde Da Ikpeazu Sun Shilla Kasar Waje, An Bayyana Dalilin Fitarsu

Gwamna Matawalle
Kotu Ta Haramtawa EFCC Kwace Wasu Manyan Kadarorin Gwamna Matawalle. Hoto daga TheCable
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake zartar da hukuncin, alkalin kotun, Justis Inyang Ekwo, ya yi amfani da sashi na 308 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya baiwa gwamnoni kariya daga fuskantar shari’a.

Hukumar EFCC a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/709/22 ta yi karar mamallakin kadarorin guda shida.

Kadarorin sun hada da Fili mai lamba 729, Idu Industrial Layout; Fili mai lamba 1327, Cadastral Zone AO5, yankin Maitama; Fili mai lamba 2934, Cadastral Zone, AO6, yankin Maitama da fili mai lamba 730, Cadastral Zone AO6, yankin Maitama.

Sauran sune fili mai lamba 28048, Cadastral Zone, yankin Maitama District, da fili mai lamba na 515, Cadastral Zone, BOO, yankin Kukwaba.

A karar da ta shigar, EFCC ta nemi a mallakawa gwamnatin tarayya filayen guda shida.

A hukuncinsa, Justis Ekwo ya bayyana cewa hukumar bata da karfin shigar da kowace kara kan Matawalle yayin da yake kan kujerar gwamna.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

Alkalin ya yarda da matsayar Ahmed Raji, SAN, wanda ya bayyana a madadin Matawalle, na cewa karar da EFCC ta shigar kan gwamnan cin mutuncin kotu ne duba ga kariyar da doka ta bashi.

A ranar 26 ga watan Mayu, Ekwo ya kwace kadarorin na wucin gadi a wani hukunci da ya zartar, amma kuma ya janye hukuncin a yanzu.

Alkalin ya bayyana cewa hukumar yaki da rashawar bata da hurumin neman a kwace kadarar wani gwamna mai ci.

Muna Binciken Matawalle Kan Amfani Da Kudin Al'umma Wajen Siyan Gidaje a Abuja, EFCC

A wani labari na daban, Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tace tana binciken gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle bisa zargin almundahana.

EFCC tace ta fara binciken gwamnan ne sakamakon bayanan da ta samu na cewa yana amfani da dukiyar al'ummar jiharsa wajen mallakan kadarorin biliyoyi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel