Mazaunin Gidan Haya Ya Sace Mai Gidan Tare da Karɓar Naira Miliyan 1

Mazaunin Gidan Haya Ya Sace Mai Gidan Tare da Karɓar Naira Miliyan 1

  • Haɗa baki dai da masu garkuwa da mutane a wasu jihohi na cigaba da bazuwa
  • Wani mutum ne ya haɗa baki da masu garkuwa da mutane tare da karbar naira miliyan ɗaya
  • Rundunar ƴan sanda ta jihar Osun ta tabbatar da kame huɗu daga cikin masu garkuwa da mutumin

Osogbo - Jami'an rundunar ƴan sanda ne ta jihar Osun suka gano gawar wani tsoho mai suna Oladepo Asaolu wanda mamallakin gidan haya bayan kwanaki huɗu da ɓacewarsa, rahoton ChannelsTV.

Tsohon wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Ifedayo dake garin Ora-Igbomia ta jihar Osun fitaccen mutum ne a garin nasu.

Bincike ya nuna cewa, ɗaya daga cikin mazauna gidan hayarsa ne ya miƙa shi ga masu garkuwa da mutane a kan kuɗi Naira miliyan ɗaya.

Kara karanta wannan

Jinkirin Karasa Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: Gwamnatin China Ta Hana Najeriya Bashi

Sanda
Mazaunin Gidan Haya Ya Sace Mai Gidan Tare da Karɓar Naira Miliyan 1
Asali: Facebook

A ranar 5 ga watan Oktoba, 2022 ne ake zargin mai gidan hayar da ɓacewa bayan da wani mai babur ya zo ya har gidansa da ke Ora-Igbomina da misalin ƙarfe 5 na yamma tare da kai shi wani waje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mamacin dai ya sanar wa da maƙotansa cewa mai mashin ɗin dai zai kai shi ne zuwa gonarsa kafin daga bisani aka tsinci gawarsa a daji. .

Tuni dai mai magana da yawun rundunar ƴan sandan na jihar, Yemisi Opalola ya tabbatar da faruwar wannan al'amari.

Yace:

"Da gaske, a ranar Lahadi, mun samu gawar mutumin ta fara ruɓewa a daji kuma na gano cewa, wani mutum ɗan asalin garin Osan ne ya haɗa baki da masu garkuwa da mutane a kan kuɗi Naira miliyan ɗaya.
"Sannan mun yi nasarar kama masu garkuwa da shi har mutane huɗu kuma yanzu haka suna nan a tsare".

Kara karanta wannan

Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane

An Damke Matar Aure Kan Laifin Shirya Yadda Akayi Garkuwa Da Mijinta

A wani labarin kuwa, Jami'an hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ranar Juma'a sun bayyana wata mata mai suna Joy Emmanuel wacce akewa zargin shirya yadda akayi garkuwa da mijinta, Emmanuel Ebong.

Kwamishanan yan sandan jihar, Olatoye Durosinmi, ya bayyanawa manema labarai cewa Joy tare da masu garkuwa da mutanen sun amshi N2million matsayin kudin fansa hannun mijin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel