Kano: Mun Shriya Tsaf Don Yiwa Kwankwaso da Ganduje Ritayar Dole a Siyasa, ‘Dan Takarar Gwamna a LP

Kano: Mun Shriya Tsaf Don Yiwa Kwankwaso da Ganduje Ritayar Dole a Siyasa, ‘Dan Takarar Gwamna a LP

  • ‘Dan takarar kujerar Gwamna a jihar Kano karkashin jam’iyyar LP, Bashir Ishaq Bashir yace sun shirya yi wa Kwankwaso, Ganduje da Aminu Wali ritayar siyasa a 2023
  • Ishaq ya zargi jagororin siyasar jihar Kano da nuna halin ko in kula ga damuwar al’umma wanda yace jam’iyyarsu zata magance hakan idan ta hau mulki
  • Ya kara da musanta tafe-radon dake yawo na cewa Peter Obi bashi da farin jini a arewacin Najeriya inda yace zasu shayar da mutane mamaki

Kano - Dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Kano, Mista Bashir Ishaq Bashir, ya ce jam'iyyarsa ta kammala duk wasu tsare-tsare don yiwa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Ambasada Aminu Wali ritaya daga siyasa a 2023.

Kara karanta wannan

Rikici: An farmaki hadimin Ganduje a Kano, ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka sace wayarsa

Bashir Ishaq da Peter Obi
Kano: Mun Shriya Tsaf Don Yiwa Kwankwaso da Ganduje Ritayar Dole a Siyasa, ‘Dan Takarar Gwamna a LP. Hoto daga Leadership
Asali: Facebook

Jaridar Thursday ta rahoto cewa Bashir, wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kano, ya zargi shugabannin da nuna halin ko-in kula da damuwar mutane, yana mai cewa yan siyasar uku sun kasance jagororin jam'iyyunsu kuma masu fada aji a siyasar Kano.

A cewarsa, tawagar kamfen dinsa ta hada kwararru wadanda ke da gogewar da zasu iya dawo da martabar Kano a matsayin cibiyar kasuwancin arewa, Leadership ta rahoto.

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"A cikin shukaru 20 da suka gabata, mun samu shugabanni da suka hau karagar mulki babu shiri. Shugabanninmu basu damu da damuwar mutane ba. Za mu tabbatar da ganin cewa Kano ta girmama a bangaren tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Zata Ba Mutane Mamaki a Zaben Shugaban Kasa Na 2023, Kwankwaso

"A kowace al'umma da kuma cikin mawuyacin lokaci, ana samun wata tawaga da ke kunshe da mutane masu kishi da son ci gaban al'ummarsu.
"Wadannan mutane sune masu hangen yadda ya kamata al'ummarsu ta kasance da kuma yadda bai kamata ta kasance ba. Mutane masu halayen kwarai wadanda babu shakku a kokarinsu na yiwa mutane hidima. Maza da mata masu sadaukar da son ransu saboda mutanensu. "

Ya kuma yi watsi da rade-radin cewa Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa, Peter Obi bai da farin jini a arewa, yana mai cewa lallai LP za ta shayar da mamaki a Kano dama arewa baki daya duba ga yadda take kara karfi.

Peter Obi Ya Yi Magana a Kan 'Hada-Kai' da Atiku Bayan An yi Kus-Kus a Landan

A wani labari na daban, Ofishin yada labaran kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Obi-Datti 2023, sun ce babu wata magana da aka ajiye da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitaccen Dan Siyasa Kuma Na Kusa da Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Rasu

A ranar Lahadi, Vanguard ta rahoto cewa kwamitin neman zaben takaran Obi-Datti 2023 ya fitar da jawabi game da rade-radin marawa PDP baya a zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel