Abin da Ya Sa Gwamnatin Tarayya Ta Saki ‘Yan Boko Haram 100 Daga Kurkuku a Boye

Abin da Ya Sa Gwamnatin Tarayya Ta Saki ‘Yan Boko Haram 100 Daga Kurkuku a Boye

  • Ana yada jita-jita cewa gwamnatin tarayya ta ba wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da ke daure ‘yanci
  • Rade-radin da ke yawo shi ne an saki tsofaffin mayakan ne ceto fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja
  • Majalisar tsaro ta kasa tayi karin haske a kan lamarin, babu gaskiya a maganganun da mutane suke yi

Lagos - Sasantawa da aka yi a wajen kotu ne ya yi sanadiyyar da aka fito da mutane 101 da ake zargin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram ne a Najeriya.

Wani dogon rahoto da ya fito daga Daily Trust ya bayyana cewa mutum fiye da 100 da ke tsare a gidan gyara halin Kirikiri da ke Legas sun samu ‘yanci.

Akwai masu yada jita-jita cewa an saki wadannan mutane ne a matsayin musanya da aka yi da su da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka dauke.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

Daily Trust Saturday ta samu labari daga majiyoyi masu karfi cewa tuni aka fara sakin wadannan mutane da ke tsare, akasin abin da mutane ke fada.

Karin hasken Janar Lucky Irabor

Bayan taron majalisar tsaro na kasa da aka yi a Abuja, shugaban hafsun tsaro na kasa, Janar Lucky Irabor ya shaidawa ‘yan jarida gaskiyar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji
Majalisar tsaro na kasa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC
"Watakila a wannan gaba akwai bukatar in ce an yi wa majalisa (NCS) bayani a kan tsofaffin mayaka 101 da aka kai su Operation Safe Corridor (a Gombe).
Yanzu haka ana cire masu zafin kishin addini a wannan cibiya. Wadannan tsofaffin mayaka da sun yi shekaru a daure, sun yi zamansu a gidan kaso.
Saura su ne masu jiran kotu, amma saboda lokacin da abin yake dauka wajen irin shari’arsu, yadda ake bi shi ne a dauke su domin cire masu zafin addini."

Kara karanta wannan

Buhari Ya Amince a Raba Buhunan Kayan Abinci 240, 000 a Wuraren da Aka Yi Ambaliya

- Janar Lucky Irabor

Yadda aka cin ma matsaya a shari'a

Karin bayanin jaridar ya nuna cewa gwamnati ta bakin babban Lauyan gwamnati ta shiga yarjejeniya majalisar lauyoyi kafin daukar wannan matsaya.

A watan Oktoban nan Alkali Awogboro Olawunmi, Tijjani Garba Ringim da Nicholas Oweibo duka suka zartar da hukunci cewa a saki fursunonin su 101.

Gaskiyar maganar ita ce an kama wasu daga cikin ‘yan ta’addan tun a 2009 a garuruwan Bauchi, Maiduguri da Kano, tun a lokacin suke garkame.

Saboda haka ba gaskiya ba ne a ce sun samu ‘yanci ne domin a kubutar da fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna wadanda suka yi watanni shida a cikin jeji.

Chimamanda Ngozi Adichie ba ta son OFR

Dazu kun ji labari Chimamanda Ngozi Adichie tana cikin wadanda aka ware za a ba lambar karramawa a 2022, amma ta ki yarda ta karbi lambar yabon.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Tsirara Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna

Shahararriyar marubuciyar ba ta gamsu da wannan ba, ta ki yarda ta karbi lambar girman kamar yadda Farfesa Chinua Achebe ya yi a lokacin rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel