Yadda Shahararriyar Marubuciya Tayi Watsi da Lambar Girmamawan Gwamnatin Buhari

Yadda Shahararriyar Marubuciya Tayi Watsi da Lambar Girmamawan Gwamnatin Buhari

  • Chimamanda Ngozi Adichie tana cikin wadanda aka ware za a ba lambar karramawa a 2022
  • Da alama shahararriyar marubuciyar ba ta gamsu da wannan ba, ta ki yarda ta karbi lambar girman
  • Amma Chimamanda Ngozi Adichie tayi hakan ne ba tare da ta filo fili ba, saboda gudun bakin jama’a

Abuja - Mashahuriyar marubuciyar Duniya, Misis Chimamanda Ngozi Adichie ba ta karbi lambar girmamawa daga hannun gwamnatin Najeriya ba.

Binciken da The Guardian tayi, ya tabbatar da Chimamanda Ngozi Adichie tayi watsi da lambar girman da aka shirya za a ba ta tare da wasu 'yan kasa.

Daya daga cikin ma’aikatan marubuciyar, Omawumi Ogbe ya shaidawa jaridar cewa Chimamanda Adichie mai shekara 45 tayi watsi da karramawar.

"Bayan Shugaban kasa ya bada lambobin girma, rahotanni masu cin karo da juna suna yawo a kan daya daga cikin wadanda za a karrama, Chimamanda Ngozi Adichie.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

Wasu sun ce marubuciyar Duniyar ta karbi lambar, wasu kuma sun ce ba ta karba ba. Marubuciyar ba ta karbi wannan kyauta ba, saboda haka ba ta halarci taron ba.
Amma kuma ba ta so wannan lamarin ya jawo mata abin magana, saboda haka ta ki karbar karramawar ne a boye."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Omawumi Ogbe

Chimamanda Adichie
Chimamanda Adichie da Shugaban kasa Hoto: brittlepaper.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta tabbatar da wannan labari, tace Chimamanda Ngozi Adichie ta zabi tayi watsi da wannan lamba na girma ba tare da tallata matsayar ta ba.

An nemi Chimamanda Adichie ba a gani ba

Legit.ng Hausa ta fahimci mutane sun yi ta magana ganin cewa ba a ga Adichie a wajen bikin ba, wasu sun yi tunani ta aika wakili ne saboda ta gaza halarta.

A cikin matan da aka gwamnatin Muhammadu Buhari ta karrama akwai Dr. Ngozi Okonjo Iweala da Ms. Amina J. Mohammed wanda suka karbi lambar GCON.

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: Majalisar Tsaron Najeriya Ta Yi Karin Haske Kan Shugaban IPOB, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Rahotonni sun ce tun farko Adichie wanda kwanan nan aka karrama ta da lambar W.E.B. Du Bois a Amurka ba ta taka kafa zuwa Aso Villa inda aka yi bikin ba.

Ba yau aka fara ba

Kafin marubuciyar, an yi Farfesa Chinua Achebe wanda shi ma marubuci ne da aka nemi a ba shi irin wannan lambar karramawa, amma ya ki yarda ya karba.

Kun ji labari Gani Fawehinmi SAN, Lauya mai kare hakkin Bil Adama ya ki karbar lambar girman OFR a lokacin da gwamnatin Yar’Adua ta nemi karrama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel