Hana Sallar Juma'a: Musulmi Sun Fara Zuwa Bankin Polaris Suna Rufe Asusun Ajiyarsu

Hana Sallar Juma'a: Musulmi Sun Fara Zuwa Bankin Polaris Suna Rufe Asusun Ajiyarsu

  • Mutane a dandalin sada zumunta na Twitter musamman musulmi na cigaba da ragargazan bankin Polaris kan sakon hana zuwa sallar Juma'a da wata manaja ta tura wa ma'aikata
  • Biyo bayan sakon, Bankin Polaris ya fitar da sanarwa ya ce ma'aikaciyar ta tura sakon kan jahilci ne kuma za a warware matsalar a cikin gida
  • Amma duk da hakan, wasu mutane sun fara zuwa bankin don rufe asusunsu tare da shawartar wasu su yi hakan don kishin addinin musulunci duba da cewa ba su gamsu da matakin da bankin ya dauka ba

Twitter - Daya daga cikin bankunan kasuwanci a Najeriya, Polaris Bank, na cigaba da shan suka da bore daga wasu musulmin Najeriya kan hana ma'aikata zuwa sallar Juma'a da wata manaja ta yi a sashinta.

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

A wani sakon imel da ya fito, wata ma'aikaciya mai suna Damilola Adebara ta ce bankin ba shi da tsarin kyalle ma'aikata zuwa ibada a lokacin aiki.

Bankin Polaris.
Hana Sallar Juma'a: Musulmi Sun Fara Zuwa Bankin Polaris Suna Rufe Asusun Ajiyarsu. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Imel din ya nuna cewa ma'aikatan na aiki ne a cibiyar YES na bankin, sashin kula da kwastomomi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bankin Polaris ya bada hakuri

Sai dai tuni bankin ya fitar da sanarwa yana mai bada hakuri tare da cewa manajan da ta tura sakon ta yi hakan ne bisa jahilci amma ba tsarin bankin bane.

Bankin na Polaris a sakon bada hakurin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya kuma ce za a warware matsalar a cikin gida.

Sai dai bisa alamu hakan bai gamsar da wasu mutane ba musamman musulmi inda suka sha alwashin daukan mataki kan bankin.

Wasu sun zargi bankin da rashin girmama addinin musulunci don haka ba za su cigaba da yin harka da bankin ba, wasu sun yi kira ga musulmi su kauracewa bankin.

Kara karanta wannan

Wani Bankin Najeriya Na Shan Zafaffan Suka Saboda Wasikar Hana Ma'aikata Zuwa Sallar Juma'a

Wasu masu amfani da Twitter sun sha alwashin rufe asusunsu da Polaris da na yan uwansu

Wani mai yawan sharhi kan al'amuran yau da kullum a Twitter, mai suna Sarki (@Waspapping_) ya ce lokaci ya yi da musulmi za su kaurace wa bankin Polaris.

Kalamansa:

"Lokaci ya yi da musulmi za su kauracewa bankin Polaris."

Ya kara wani rubutun da cewa:

"Kauracewa bankin Polaris da musulmi ke yi zai zama darasi ga wasu kamfanoni masu zaman kansu da su rika girmama musulmi da addininsu."

Hakazalika ya ce da izinin Allah zai tafi bankin na Polaris ranar Litinin ya rufe asusunsa.

Wani mai amfani da Twitter, Engr Abdooll (@khamees_abdooll) ya wallafa hoto yana mai nuni da cewa musulmi da dama sun tafi bankin Polaris suna rufe asusun ajiyarsu.

Kalamansa:

"Kwastomomi musulmi sun yi tururuwa zuwa Bankin Polaris don kwashe kudinsu tare da rufe asusun bankinsu.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida: Ba Za Mu Sake Yarda Da Wani Zabe Na 'Inconlusive' Ba A Kano

"Dalili?"

Wani duk dai a Twitter mai suna Sambo Mai Hula (@Abdullahiabba_), a shafinsa ya nuna cewa zai umurci mahaifiyarsa ta rufe asusunta da bankin.

Ya ce:

"Gobe da safe idan na dawo gida da izinin Allah za tilasta wa mahaifiyata ta rufe asusunta da ke Bankin Polaris sannan a ranar Litinin zan tafi in cire dukkan kudin ta da izinin Allah."

Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna Kawu Garba (@KawuGarba) ya ce:

"Sanarwar da bankin Polaris ya fitar ya yi ikirarin ma'aikaciyar da ta tura sakon hana ma'aikata musulmi zuwa sallar Juma'a ba da izinin bankin ta yi ba. Ba labari bane kawai tunda ba a kore ta ba?
"Wannan mutane ba su dauke mu komai ba."

Wani Bankin Najeriya Na Shan Zafaffan Suka Saboda Wasikar Hana Ma'aikata Zuwa Sallar Juma'a

Tunda farko kun ji cewa, daya daga cikin manyan bankunan kasuwanci, Polaris Bank, na shan suka bayan daya daga cikin manyan ma'aikatansa ta umurci na kasa da ita kada su tafi sallar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikici: Tashin hankali yayin da kanin miji ya kwace wa dan uwansa mata mai 'ya'ya 7

A wani imel da ya fito, daya daga cikin ma'aikatan bankin, Damilola Adebara, ta ce bankin ba shi da tsarin barin ma'aikata su tafi ibada a lokacin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel