Wani Bankin Najeriya Na Shan Zafaffan Suka Saboda Wasikar Hana Ma'aikata Zuwa Sallar Juma'a

Wani Bankin Najeriya Na Shan Zafaffan Suka Saboda Wasikar Hana Ma'aikata Zuwa Sallar Juma'a

  • Bankin Polaris a Najeriya na shan suka saboda wata wasika da shugaban wani sashi a bankin ta tura wa na kasa da ita na hana su zuwa sallar Juma'a don yana shafar aiki
  • Bankin ya fitar da sanarwa ya ce ma'aikaciyar da ta tura wasikar ta yi hakan ne kan jahilci ne kuma ya saba wa tsarinta
  • Bankin ta kuma ce za a warware batun ta cikin gida tana mai jadada wa al'umma cewa tana mutunta damar da kowanne ma'aikaci ke da shi na yin addinin da ya so

Daya daga cikin manyan bankunan kasuwanci, Polaris Bank, na shan suka bayan daya daga cikin manyan ma'aikatansa ta umurci na kasa da ita kada su tafi sallar Juma'a, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da aka ga bidiyon mata mai juna biyu na leburanci a wurin wani gini

A wani imel da ya fito, daya daga cikin ma'aikatan bankin, Damilola Adebara, ta ce bankin ba shi da tsarin barin ma'aikata su tafi ibada a lokacin aiki.

Banki
Wani Bankin Najeriya Na Shan Suka Saboda Wasikar Hana Ma'aikata Zuwa Sallar Juma'a. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sakon na imel ya nuna cewa ma'aikatan na aiki ne a sashin Cibiyar YES, wani bangare na bankin.

Wani sashi na imel din ya ce:

"An lura cewa a ranar Juma'a, kana barin aikinka ka tafi sallar Juma'a duk da sani abin da rashin ka zai janyo ga aiki a Cibiyar Yes."
"Ka sani cewa babu wani wuri a tsarin aikin bankin da ya bawa ma'aikata damar tafiya ibada a lokacin aiki. Daga yanzu ba za a rika amincewa da haka ba a Cibiyar Yes kuma duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci. Ana sa ran kowa ya amsa cewa ya ga wannan sakon. Na gode."

Kara karanta wannan

Araha bagas: Yadda budurwa ta dauki kaninta ta kaishi karatu Cotonou, ta biya N210k

Bankin ta ce ba da yawunta ma'aikaciyar ta tura wannan sakon ba

Da bankin ke martani kan wasikar, ta ce abin da ma'aikaciyar ta tura a wasikar ba ya tsarin bankin.

Yayin da bankin ke jadada cewa Najeriya ba kasa ce da ke da wani addini a hukumance ba, bankin ba shi da tsarin hana ma'aikata yin addininsu.

"An janyo hankalin bankin kan wani hoton wasikar imel da mai kula da ita ta tura musu a sashin su dangane da zuwa sallar Juma'a.
"Muna son fayyace cewa Najeriya ba kasa bace mai bin wani addini a hukumance kuma bankin mu yana bin wannan tsarin. Don haka, babu wani tsari a bankin da ya hana ma'aikaci yin addinin ya da so; don haka ma'aikaciyar ta dauki matakin bisa jahilci kuma mun warware batun a cikin gida."
"Muna tabbatar wa ma'aikata, kwastomomi, da dukkan al'umma cewa za mu cigaba da girmama damar da kowane ma'aikaci ke da shi na yin addininsa."

Kara karanta wannan

Bidiyon malamin makarantan da ya tafi banki da 'Ghana Must Go' don karbo albashinsa

Abin da wasu mutane suka ce kan martanin bankin

Wani mai amfani da Twitter Coolex ya ce:

"Wannan bankin (Polaris) ba ya son musulmi. Ma'aikaciya ta rika barazana ga na kasa da ita cewa kada su tafi sallar Juma'a. Damilola I. Adebara musulmi na kalon ki. An hallice mu ne don bauta wa Allah ba Polaris ba."

Yusuf Shehu Ahmodu ya ce:

"Haka lamarin ya ke a bankunan Najeriya illa Zenith da Union Bank."
"Ya faru lokacin da na ke aiki a Diamond Bank. Sai na rusuna ina rokon mai kula da ni kafin ta kyalle ni in tafi inyi sallah."

Ismaeel Musa ya ce:

"Ina daf da bada shawara, musamman ga musulmi, kada su saka jari ko kasuwanci da duk wani banki wanda bai kare hakkin ma'aikata (musulmi da kirista)."

Habibu Bawa ya ce:

"Rashin sani ba uzuri bane, wane mataki aka dauka ka/ko za a dauka kan shugaban bisa abin da ta aikata kan jahilci?".

Asali: Legit.ng

Online view pixel