Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Buhari Ya jaddada

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Buhari Ya jaddada

  • Shugaba Buhari ya jaddadacewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen magance matsalar tsaro
  • Buhari ya baiwa jami'an tsaro wa'adin kawar da yan bindiga da masu garkuwa da mutane nan da Disamba
  • Kimanin mutane 443 aka bawa lamabar yabon girmamawa jiya ciki harda malaman addini da mawaka da dai wasu dai-daiku

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyarsa tabattarwa da ‘yan Najeriya danka mulki ga wanda zai gaje shi ba tare da wata matsalar tsaro ba kamar yadda ya bayyana a bikin bayar da lambar girma ga wasu ‘yan kasa.

"Zamu ci gaba da yakar duk wasu nau'in bata gari masu aikata laifuka da ta'addanci a fadin kasa nan.

Kara karanta wannan

Za'a magance dukkan matsalolin tsaron Najeriya nan da watan Disamban, Gwamnati

Kamar yadda shugaban ya bayyana hakan tun farko a jawabin ranar samun yan cin kai, zan mikawa ‘yan Najeriya zuwa ga wanda zai gajeni, da kyakkawan tsarin rashin tsaro da zaman lafiya,”

...Inji shi.

Buhari kuma ya kara da cewa lambar girmamawa ba wata lamba bace ta ado ba, a’a wata alama ce ta kara dagewa mutum ganin ya ci gaba da iyukan bunkasa ta re tabbatar da zaman Nijeriya daya.Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki

Buhari
Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Buhari Ya jaddada Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin cewa a cikin sauran kwanakin da suka rage masa a matsayin shugaban ƙasa, ƴan Najeriya za su ga sauyi game da matsalar tsaro.

Shugaban ya ba da wannan tabbaci ne a ranar Juma’ar nan da yake gabatar wa da Majalisar ƙasa tsararren jadawalin kasafin kuɗin Naira tiriliyan ashirin da dubu ɗari biyar da hamsin da ɗaya.

Najeriya dai ta daɗe tana shan fama game da matsalolin tsaro da ya haɗa da na Boko Haram a Arewa maso Gabas da na tsaginta, wato ISWAP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel