Kasafin Kudi: Buhari Ya Fadawa Majalisa Ba Zai Cigaba da Biyan Tallafin Fetur a 2023 ba

Kasafin Kudi: Buhari Ya Fadawa Majalisa Ba Zai Cigaba da Biyan Tallafin Fetur a 2023 ba

  • Muhammadu Buhari ya nuna gwamnatin tarayya tana kashe makudan kudi a kan tallafin man fetur
  • Shugaban Najeriyan yake cewa gwamnatinsa ta batar da N1.5tr a cikin watannin shidan farkon 2022
  • Ganin kudin da suke bacewa da nufin a tsaida farashin litar fetur, zai yi wahala a iya tafiya a haka

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya koka a kan yadda ake batar da makudan biliyoyin kudi a wajen biyan tallafin man fetur a Najeriya.

Yayin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2023, Daily Trust ta rahoto Muhammadu Buhari ya na wannan kuka da ya je gaban majalisa.

Ganin halin da kasar take ciki a halin yanzu, Shugaban Najeriyan yace ba zai yiwu a cigaba da batar da makudan kudi a kan tallafin man fetur ba.

Kara karanta wannan

Bakano ya girgiza intanet, ya kera keke napep din da ta ba 'yan Najeriya mamaki

“Ana ta biyan tallafin man fetur duk shekara, kuma tun farkon shekarun 1980 ake ta aiki da wannan tsari.
Amma irin kudin da ake batarwa ya nuna cewa tabbas wannan tsari ba zai daure a haka ba.”
“A matsayinmu na kasa, dole mu magance wannan matsalar domin akwai bukatar a rage radadin da al’umma suke ciki.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari a Majalisa Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Da yake bayani a game da kasafin kudin shekarar badi, Buhari yace a duk rana gangunan danye man fetur miliyan 1.3 Najeriya ke hakowa.

Zuwa Yunin 2022, Buhari yace gwamnatin tarayya ta kashe abin da ya kai Naira Tiriliyan 1.59 wajen biyan tallafin man fetur a shekarar nan.

An batar da kudin nan ne daga farkon watan Junairun shekarar 2022 zuwa watan Yunin nan.

Jawabin shugaban kasar ya na nuna da wahala gwamnatin tarayya ta ware kudi domin a rika biyan tallafin man fetur ga 'yan kasuwa a 2023.

Kara karanta wannan

Biliyoyin da Shugabanni Suka Wawure Daga Najeriya Suna Dankare a Turai, Buhari

Satar danyen mai

Kun ji labari Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPC) tace an shafe sama da shekaru 20, tsageru suna sace danyen man kasar nan.

Malam Mele Kolo Kyari yace barna mafi muni ita ce wani dogon bututu da aka kafa, aka yi shekaru 9 ana satar mai ta teku da suka gano a kwanaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel