Za a sa Kafar Wando Daya: Gwamnati Za Ta Karbe Obajana Daga Hannun Dangote

Za a sa Kafar Wando Daya: Gwamnati Za Ta Karbe Obajana Daga Hannun Dangote

  • Gwamnatin Kogi tayi bincike a kan saida kamfanin simintin Obajana da aka yi a shekarun baya
  • Binciken da SSG ta gudanar ya nuna ba Dangote Industries Limited suke da mallakar kamfanin ba
  • Ana zargin an saba doka wajen sayen kamfanin simintin, kuma majalisar Kogi ba ta san da cinikin ba

Kogi - Gwamnatin jihar Kogi tace ta soma shirin karbe kamfanin simintin da ke Obajana daga hannun kamfanin Dangote Industries Limited.

A ranar Larabar nan aka rufe kamfanin simintin saboda sabani a kan hakkin mallaka. The Cable ta fitar da wannan rahoto a yammacin jiya.

Wani rahoto da aka gabatarwa Gwamnan jihar Kogi, ya nuna Gwamnati ba ta yarda kamfanin simintin Dangote ya mallaki kamfanin Obajana ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Neman Zabe Ya Kare Tsakanin Mutanen Tinubu da Shugabannin Jam’iyyar APC

A rahoton da Sakatariyar gwamnatin jihar, Folashade Ayoade ta gabatar, ta nuna cinikin Dangote da kamfanin simintin Obajana bai tabbata ba.

SSG tace satifiket din da kamfanin ya yi amfani da su a lokacin yana karkashin Jihar Kogi ne Aliko Dangote ya yi aiki da su wajen cin bashin N63bn.

Ayoade tace kwamitinta da ya yi bincike a kan lamarin ya bada shawara ga gwamnatin Kogi ta karbe kamfanin daga hannun Alhaji Dangote.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obajana
Kamfanin Obajana Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Rahoton yace sakatariyar gwamnatin ta jagoranci kwamitin da ya fadawa gwamnati ta karbe har da ribar kudin da Dangote ya rika samu daga Obajana.

Shawarar kwamitin Folashade Ayoade

“Babu shaidar da ke nuna Dangote Industries Limited ya biya jihar Kogi kudi wajen mallakar kamfanin Obajana Cement Company Plc.
Babu kudin da aka biya jihar a matsayin ribar da aka samu daga lokacin a kamfanin Dangote Cement Company ya fara aiki zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kama babban dan kasuwa a Najeriya da laifin shigo da kwayoyin Tramadol

Satifiket din mallaka uku na kamfanin Obajana Cement Company Plc sun tabbatar da gwamnatin Kogi ce kadai take da hakkin mallaka.”

- Folashade Ayoade

Majalisa ba ta san ciniki ya fada ba

Daily Nigerian ta rahoto shugaban majalisar dokokin Kogi, Matthew Kolawole yana cewa an saida kamfanin ne ba tare da sanin ‘yan majalisar jihar ba.

Kolawole yace ba za a iya saida dukiyar gwamnati ba tare da sa bakin majalisar dokoki ba, don haka an saba doka wajen saida hannun jarin Obajana.

Abin ya kai ga harbe-harbe

A dalilin haka ne Legit.ng Hausa ta samu labari an tura ma’aikata da jami’an tsaro su rufe kamfanin, wanda hakan ya yi sanadiyyar harbe wasu direbobi.

Wasu ma'aikatan kamfanin sun shaida mana mutane bakwai sun samu rauni, kuma an harbe wasu. Yanzu haka suna jinya a asibitin kwararru a Lokoja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel