Mutane 3 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Farmaki Borno

Mutane 3 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Farmaki Borno

  • Yan Boko Haram sun kai hari garin Njilang, karamar hukumar Chibok na jihar Borno da tsakar dare
  • Mayakan sun yi ta harbi kan mai uwa da wahabi inda suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu da dama
  • Yan ta’addan fasa shaguna inda suka yi sace-sace kafin suka cinnawa gidan jama’a wuta

Borno - Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kashe akalla mutum uku a wani sabon farmaki da suka kai garin Njilang da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.

Wata majiya ta tattabatar da faruwa lamarin ga Channels TV a wata hira ta wayar tarho a ranar Talata, 4 ga watan Oktoba.

Majiyar ta ce mayakan sun farmaki sabuwar hanyar Maiduguri –Damboa da aka bude kwanan nan a tsakar daren yau Talata.

Kara karanta wannan

Bayan Watanni Uku, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Fursunonin da Suka Gudu Daga Gidan Yarin Kuje

Jihar Borno
Mutane 3 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Jikkata Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Farmaki Borno Hoto: Channels tv
Asali: UGC

A yayin kai harin, an kona gidaje da dama yayin da mazauna yankin da dama suka jikkata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa mayakan sun dana bama-bamai a kan titin da ya lalace lokacin da wata babbar mota ke wucewa da kayan abinci.

Majiyar ta ce:

“Mayakan sun farmaki Njilang da misalin karfe 2:34 na tsakar daren Talata sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi, a cikin haka ne mutane uku suka mutu sannan suka yi sace-sace a shaguna kafin suka cinnawa gidajen jama’a wuta ba tare da tangarda ba.
“Mayakan sun shirya gadar zare ne kan wasu motoci da ke dauke da kayan abinci inda suka yi nasara wajen aiwatar da nufinsu.”

Shugaban karamar hukumar Chibok, Umar Ibrahim, ya kuma tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce:

“Ina sane da lamarin da ya faru a Njilang saboda a karamar hukumata take kuma abun bakin ciki ne cewa Chibok ta shahara saboda dalilai marasa dadi.

Kara karanta wannan

Idan Na Siya Dankareriyar Mota Kada Kuyi Mamaki, Budurwa ‘Yar Najeriya Da Ke Sana’ar Jari Bola

“Daya lamarin na bam ba a Chibok bane, nima dai na ji ne daga wajen mutanen da suka tuntubeni.”

Bayan Watanni Uku, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Fursunonin da Suka Gudu Daga Gidan Yarin Kuje

A wani labarin, mun ji cewa har yanzu ba a kamo fiye da fursunoni 422 da suka tsere daga magarkamar Kuje da ke Abuja a ranar 5 ga watan Yulin 2022 ba, Sahara Reporters ta rahoto.

Idan za ku tuna, fursunoni 879 ciki harda manyan yan ta’addan Boko Haram ne suka tsere daga magarkamar a yayin wani farmaki da yan bindiga suka kai gidan yari.

Kakakin hukumar gidan gyara hali ta kasa, Umar Abubakar, ya ce mutum biyar da suka hada da wani jami’in NSCDC da fursunoni hudu ne suka mutu a lokacin hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel