Mijina Ya Kwashe Shekaru Da Dama Yana Fama Da Ciwon PTSD, Aisha Buhari

Mijina Ya Kwashe Shekaru Da Dama Yana Fama Da Ciwon PTSD, Aisha Buhari

  • Uwargidar shugaban kasa ta bayyana yadda tayi jinyar mijinta shugaba Buhari tun tana yar shekara 19
  • Aisha Buhari ta caccaki yan siyasan da ke nuna fushinsu kawai don sun fadi zaben fidda gwani
  • Kungiyar matan jami'an Sojoji na shirin kafa cibiyar kula da ciwon PTSD ga mazajensu dake zuwa faggen fama

Uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari, a jiya ta bayyana cewa mijinta ya yi fama da ciwon Post Traumatic Stress Disorder (PTSD) na tsawon shekaru da dama biyo bayan abubuwan da ya fuskanta.

Ciwon PTSD wani hali da ne da mutanen da suka fuskanci rayuwa mai tsanani ke shiga daga baya. Jami'an tsaron da suke je yaki, wadanda suka dade hannun masu garkuwa da mutane, yan matan da aka yiwa fyade duk na iya shiga cikin wannan hali.

Kara karanta wannan

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

Aisha Buhari tace mijinta ya yi yakin Basasa, sannan kuma akayi masa juyin mulki, sannan kuma aka garkameshi a kurkuku tsawon watanni 40 ba tare da ya aikita wani laifi ba.

Ta ce tana yar shekara 19 lokacin kuma haka ta zama masa mai kula tsawon shekaru.

Aisha Buhari
Mijina Ya Kwashe Shekaru Da Dama Yana Fama Da Ciwon PTSD, Aisha Buhari hoto: Aisha Muhammadu BUhari
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Uwargidar shugaban kasan ta bayyana hakan ne a taron kaddamar da ginin cibiyar kula da Sojoji masu fama da PTSD da kungiyar Matan Sojoji da Yan sandan karkashin jagorancin Mrs Lucky Irabor, rahoton ThisDay.

Aisha ta caccaki yan siyasan dake kokarin tada tarzoma kawai don sun fadi zaben fidda gwani.

A kalamanta:

"A matsayina na matar Soja kuma masaniyar ilmin kula, na san kalubalen dake tattare da ciwon PTSD da kuma tasirin da yake kan iyalan Sojoji da kasa baki daya."

Kara karanta wannan

Lambar Girma: Yadda Ake ta Surutu Yayin da Manyan Na-kusa da Buhari Suka Tashi da Matsayi

"Mijina yayi aikin Soja tsawon shekaru 27 kafin akayi masa juyin mulki. Yayi yakin Basasa tsawon watanni 30 ba tare da kula ba, ya mulki Najeriya tsawon watanni 20 sannan kuma aka garkameshi tsawon watanni 40 ba tare bayyana laifin da yayi ba."
"Shekara daya da sakinsa ya aureni, ina yar shekara 19 a gidansa lokacin, saboda haka na sha wahalan illan PTSD saboda ian yar shekara 19 na kula da tsohon shugaban kasa soja."

Aisha ya ta kara da cewa cibiyar kula da masu fama da PTSD na da muhimmanci ga Sojoji saboda sun fi kowa fama da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel