Bayan Watanni Uku, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Fursunonin da Suka Gudu Daga Gidan Yarin Kuje

Bayan Watanni Uku, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Fursunonin da Suka Gudu Daga Gidan Yarin Kuje

  • Akalla fursunoni 422 da suka arce daga kurkukun Kuje a lokacin harin ranar 5 ga watan Yuli sun ki dawowa
  • Mai magana da yawun hukumar gidan yari, Abubakar Umar, ya ce har yanzu ana gudanar da mayyar farautar fursunonin da suka ci na kare
  • Umar ya kuma bayar da tabbacin cewa nan kusa za su kamo dukkanin wadanda suka tsere sannan su mayar dasu gurabensu

Abuja - Har yanzu ba a kamo fiye da fursunoni 422 da suka tsere daga magarkamar Kuje da ke Abuja a ranar 5 ga watan Yulin 2022 ba, Sahara Reporters ta rahoto.

Idan za ku tuna, fursunoni 879 ciki harda manyan yan ta’addan Boko Haram ne suka tsere daga magarkamar a yayin wani farmaki da yan bindiga suka kai gidan yari.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara Ce: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Ga Bidiyon Atiku Na Tika Rawa Da Na Tinubu Na Tuka Keke

Kakakin hukumar gidan gyara hali ta kasa, Umar Abubakar, ya ce mutum biyar da suka hada da wani jami’in NSCDC da fursunoni hudu ne suka mutu a lokacin hari.

Magarkamar Kuje
Bayan Watanni Uku, Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Fursunonin da Suka Gudu Daga Gidan Yarin Kuje Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jim kadan bayan nan, sai kungiyar ta’addanci na ISWAP ta fito ta dauki alhakin kai harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahotanni sun nuna cewa an kamo akalla mutum 32 cikin 454 da suka tsere tsakanin 15 ga watan Yuli da 3 ga watan Oktoban 2022.

A wata hira da yayi da jaridar Punch a ranar Litinin, kakakin hukumar gidan yarin ya ce har yanzu ana nan ana farautar fursunonin da suka tsere kuma nan ba da jimawa ba za a kamo dukkansu.

Umar yace:

“Sai dai fursononin da suka tsere daga hannunmu sannan suka zama fursunoni a gidajensu, duk sai mun kama su idan suka fito waje saboda akwai bayanan kowannensu a na’urar kwanfuta.”

Kara karanta wannan

Yan Fashi Sun Kutsa Coci, Sun Lakada Wa Dattawa Duka, Sun Kwashe Kudade Da Wayoyin Salula A Wata Jihar Arewa

Da aka tambaye shi kan yawan wadanda aka sake kamawa sakamakon hadakar jami’an tsaro a cikin kwanaki 30 da suka gabata, Umar yace:

“Tsarin sake kamasu yana nan yana gudana.
“Muna hadaka da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da ganin cewa an sake kama duk wani fursuna da kuma mayar da su inda ya kamata. Nan ba da dadewa ba, za mu yi jawabi ga manema labarai kan adadin da aka kamo zuwa yanzu.”

Wani Dan Wasa a Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Kwallo

A wani labari na daban, wani matashi mai shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da yake tsaka da buga kwallo a yankin Lekki na jihar Lagas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

An tattaro cewa matashin wanda ba a tabbatar da sunansa ba yana bin kwallo ne lokacin da ya yanke jiki ya fadi.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Nemi Yafiya Daga Yan Najeriya Kan Rashin Tsaro A Kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel