Tsohon Gwamnan Bauchi da Cikakken Jerin Sababbin Lauyoyin da Suka Zama SANs

Tsohon Gwamnan Bauchi da Cikakken Jerin Sababbin Lauyoyin da Suka Zama SANs

  • Kwamitin LPPC na malaman shari’a ya amince da karin matsayin wasu Lauyoyi zuwa matsayin SAN
  • Sakatariyar kwamitin, Hajo Bello ta bada sanarwar hakan bayan wani zaman LPPC da aka yi a kotun koli
  • A tsarin aikinsu, sai Lauya ya gawurta sannan yake iya zama Senior Advocate of Nigeria (SAN) a Najeriya

Abuja - Kwamitin LPPC na ma’aikatan shari’a a Najeriya, yayi wa wasu lauyoyi 62 karin matsayi zuwa manyan lauyoyi na kasa watau SAN.

Premium Times tace Magatakardar wannan kwamiti na LPPC wanda ita ce babbar magatakardar kotun koli, Hajo Bello ta bada wannan sanarwa.

Sanarwar da Hajo Bello ta fitar a ranar Alhamis ya nuna a lauyoyin da suka yi dace da wannan karin girma akwai wasu lauyoyin hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

Abin da ake fada a shafin sada zumunta a kan ‘haduwar dolen’ Kwankwaso da Ganduje

Sylvanus Tahir da Rotimi Oyedepo ma’aikatan EFCC ne, sai Wahab Shittu wanda shi ma lauya ne da hukumar da wasu suka saba daukar shi haya.

MA Abubakar ya yi dace

Jaridar nan ta Daily Nigerian tace a cikin wadanda aka ga sunansu a jerin sababbin SANs har da tsohon gwamnan Bauchi, Mohamed A. Abubakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai Sunusi Musa mai kare hakkin Bil Adama da irinsu Yakubu Maikasuwa esq.

Lauyan da Suka Zama SANs
Sanusi Musa SAN Hoto: Adnan T/Wada , @adnanmukhtaradam.tudunwada
Asali: Facebook

Wanene SAN?

Alkalin Alkalai na kasa¸ Olukayode Ariwoola ya jagoranci zama na 154 na kwamitin PLLC ya yi, inda aka amince da karin matsayin wadannan lauyoyi.

Da farko sunayen lauyoyi 129 aka fitar, daga cikinsu ne aka zabi 62 da suka yi fice a wajen aiki. Duk wanda ya zama SAN, ya yi zarra a bangaren shari'a.

Za a rantsar da malaman shari’ar a ranar 21 ga Nuwamba a kotun koli kamar yadda aka saba. Daga ciki akwai ma’aikatan shari’a 53 da farfesoshi tara

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno APC, Gwamnonin Jam’iyya na Shirin Yi wa Bola Tinubu Zagon kasa

Jerin sababbin SAN

1. MOHAMMED ABDULLAHI ABUBAKAR, ESQ.

2. JOHNSON TARIGHO OMOPHE UGBODUMA, ESQ.

3. LAWRENCE SUNDAY OKO-JAJA, ESQ.

4. CHRISTOPHER AGBOMEIRHE SUNDAY OSHOMEGIE, ESQ.

5. SANUSI OLUGBENGA SAI’D, ESQ.

6. WAHAB KUNLE SHITTU, ESQ.

7. EMMANUEL IDEMUDIA OBOH, ESQ.

8. DIRI SAID MOHAMMED, ESQ.

9. OLADIPO AKANMU TOLANI, ESQ.

10. AYODEJI OYEWOLE OMOTOSO, ESQ

11. CHIJIOKE OGBONNA ERONDU, ESQ.

12. AJOKU KINGSLEY OBINNA, ESQ.

13. YAKUBU MAIKASUWA, ESQ.

14. HENRY ESHIJONAM OMU, ESQ.

15. DAGOGO ISRAEL IBOROMA, ESQ.

16. JOSEPH ADEMU AKUBO, ESQ.

17. GOZIE BERTRAND OBI, ESQ.

18. INAM AKPADIAGHA WILSON ESQ.

19. ABUBAKAR BATURE SULU-GAMBARI, ESQ.

20. ABIOYE ARAOYE OLOYEDE ASANIKE, ESQ.

21. SYLVANUS TAHIRU, ESQ.

22. BOLARINWA ELIJAH AIDI, ESQ.

23. TONYE TOMBERE JENEWARI KRUKRUBO, ESQ.

24. ADEREMI MOSHOOD BASHUA, ESQ.

25. KOLAPO OLUGBENGA KOLADE, ESQ.

26. SAMUEL PETER KARGBO, ESQ.

27. IFEANYICHUKWU SYLVESTER OBIAKOR, ESQ.

28. OLASOJI OLAIYA OLOWOLAFE, ESQ.

29. MUTALUBI OJO ADEBAYO, ESQ.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

30. VICTOR ODAFE OGUDE, ESQ.

31. SULAYMAN OLAWALE IBRAHIM, ESQ.

32. MUMINI ISHOLA HANAFI, ESQ.

33. TANKO TANKO ASHANG, ESQ.

34. DAMIAN OHAKWE OKORO, ESQ.

35. ANDREW MWAJIM MALGWI, ESQ.

36. ETUKWU ONAH, ESQ.

37. ADEBORO LATEEF ADAMSON, ESQ.

38. BANKOLE JOEL AKOMOLAFE, ESQ.

39. KELECHI CHINEDUM OBI, ESQ.

40. ANDREW OSEMEDUA ODUM, ESQ.

41. OKORO OKECHUKWU EDWIN, ESQ.

42. GODSON CHUKWUDI UGOCHUKWU, ESQ.

43. STEVEN ONYECHI ONONYE, ESQ.

44. IKANI KANU AGABI, ESQ.

45. MUSTAPHA SHABA IBRAHIM, ESQ.

46. MUIZUDEEN YUNUS ABDULLAHI, ESQ.

47. MAGAJI MATO IBRAHIM, ESQ.

48. SUNUSI MUSA, ESQ.

49. OLADOYIN OLUSEYI AWOYALE, ESQ.

50. ROTIMI ISEOLUWA OYEDEPO, ESQ.

51. CHUKWUDUBEM BONAVENTURE ANYIGBO, ESQ.

52. LUKMAN OYEBANJI FAGBEMI, ESQ.

53. MICHAEL JONATHAN NUMA, ESQ.

‘Yan Boko da suka samu karin girma

1. FARFESA KATHLEEN EBELECHUKWU OKAFOR

2. FARFESA MUHAMMED TAOFEEQ ABDULRAZAQ

3. FARFESA AMOKAYE OLUDAYO GABRIEL

4. FARFESA ISMAIL ADENIYI OLATUNBOSUN

5. FARFESA ABDULLAHI SHEHU ZURU

Kara karanta wannan

Akwai Sanatan PDP, amma babu Yemi Osinbajo a Kwamitin yakin zaben Tinubu

6. FARFESA JOY NGOZI EZEILO

7. FARFESA THEODORE BALA MAIYAKI

8. FARFESA OLAIDE ABASS GBADAMOSI

9. FARFESA CHIMEZIE KINGSLEY OKORIE

Abduljabbar a kotu

An ji labari Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) ya jefi Lauyansa da Alkali da cin hanci.

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara yace ya biya N2m saboda ya fito daga gidan yari. Amma Alkali mai shari’a da Lauya sun ce ba ayi haka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel