Abduljabbar Ya Samu Matsala da Sabon Lauya, Ya Zarge Sa da Karbar Cin Hancin N2m

Abduljabbar Ya Samu Matsala da Sabon Lauya, Ya Zarge Sa da Karbar Cin Hancin N2m

  • Abduljabar Nasiru Kabara yace ya ba lauyansa kudi da nufin a shawo kan Alkali, ya fito da shi daga magarkama
  • Abduljabar Nasiru Kabara yace an ba Alkali N1.3m, Lauyansa Dalhatu Shehu-Usman ya tashi da N500, 000
  • Amma Dalhatu Shehu-Usman da Alkali Ibrahim Sarki-Yola duk sun ce wannan magana sam ba gaskiya ba ce

Kano Abduljabar Nasiru Kabara wanda ake zargi da laifin batanci ya zargi Lauyansa, Dalhatu Shehu-Usman da laifin karbar cin hancin kudi daga hannunsa.

Hukumar dillacin labarai na kasa tace Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara yana tuhumar Dalhatu Shehu-Usman da karbar N2m domin ya ba Alkali rashawa.

Shehin malamin da ake kara, ya bukaci kotu tayi watsi da aka shigar a kan shi, a kuma sallame shi, sannan a umarci gwamnatin jihar Kano ta nemi afuwarsa.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarki Sanusi Ya Ragargaji Gwamnatin APC a gaban Majalisar Dinkin Duniya

“Ina rokon kotu ta karbi korafin da muka rubuta a wannan shaida a matsayin hujja a kan zargin wa’adin da nayi.

Lauyana ya same ni a kurkuku

Lauyana ya zo gidan yari, ya fada mani cewa Alkali ya umarce shi ya biya Naira miliyan 2 da nufin a wanke shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyan nawa ya fadi mani ya ba Alkali N1.3m, sai ya ba wani mutum N200,000, shi karon kansa ya dauki N500, 000."

- Abduljabar Nasiru Kabara

Abduljabbar Kabara
Abduljabbar Kabara Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

An gama sauraron kara

Lauyan masu kara, Mamman Lawan-Yusufari SAN ya gama shigar da karansa yayin da ya kira mutane hudu su bada shaida a zaman kotun da aka yi a yau.

Si kuwa Malamin da ake kara ya kawo mutum daya a matsayin shaida, sannan ya kafa hujjoji da littatafai 24 da kuma faifen karatun da ya gabatar a baya.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

Ibrahim Sarki-Yola ya karbi kudi?

Daily Nigerian tace Mai shari’a Ibrahim Sarki-Yola ya yi watsi da zargin da ake yi masa, yace bai karbi cin hanci daga hannun Lauyan malamin ko wani ba.

Ibrahim Sarki-Yola yace zai bada sanarwar ranar da kotu za ta sake yin zama domin sauraron karar.

Martanin Lauyan Sheikh Kabara

Shi ma Lauyan da yake kare Sheikh Kabara, Shehu-Usman ya shaidawa manema labarai cewa bai yi mamakin jin malamin ya jefe shi da wannan zargi ba.

Dazu Jaridar Aminiya ta rahoto Lauyan yana cewa dama can sai da wanda ake tuhuma ya samu matsala da setin lauyoyi uku da suka yunkurin kare shi.

“Wannan magana karya ce; Ni ban yi mamaki ba domin wannan halinsa ne.
“Idan an duba, ya yi makamancin irin wannan zargi a kan lauyoyinsa kafin ni. a cikinsu ma akwai wadanda ya zarga da neman matarsa.”

- Dalhatu Shehu-Usman

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jigon APC a Arewa ya tada kura a Twitter, ya ce ya ga sarauniyar Ingila a aljanna

An ci Shehi tara a kotu

Kwanakin baya aka ji labari Kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta yi zama domin sauraron karar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnatin Kano.

Alkali Emeka Nwite yace Lauyan da ya tsayawa Abduljabbar Kabara ya yi kokarin raina masa hankali, a karshe aka nemi ya biya tarar N100, 000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel