An Yanke Wa Korarren Ɗan Sandan Najeriya Ɗaurin Rai Da Rai A Legas

An Yanke Wa Korarren Ɗan Sandan Najeriya Ɗaurin Rai Da Rai A Legas

  • Babban kotu a Jihar Legas ta yanke wa wani korarren jami'in dan sanda Olalekan Ogunyemi hukuncin daurin rai da rai
  • Mai shari'a Adenike Coker ta yanke wa Ogunyemi hukuncin ne bayan samunsa da laifin bindige wani mutum da ya zo kallon kwallon kafa
  • Yayin shari'ar, masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu guda bakwai yayin da wanda aka yi kara ya gabatar da shaidu biyu

Legas - Wata babban kotun Jihar Legas, a ranar Juma'a 23 ga watan Satumba, ta yanke wa wani korarren dan sanda Olalekan Ogunyemi, daurin rai dai rai saboda kashe wani mai wanda ya zo kallon kwallon kafa, Kolade Johnson, Daily Trust ta rahoto.

Gidan Gyaran Hali
An Yanke Wa Korarren Dan Sandan Najeriya Daurin Rai Da Rai A Legas. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ogunyemi, wanda ke aiki tare da tawagar yaki da yan kungiyar asiri na yan sanda, ya bindige Johnson a cikinsu a ranar 31 ga watan Maris na 2019 a wurin kallon kwallo a Mangoro, Ikeja, Legas.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin yanke hukuncin, Mai shari'a Adenike Coker ta samu wanda aka yi karar da laifin da aka tuhume shi da shi ta kuma yanke masa hukuncin daurin rai da rai, inda ta ce dole ya yi a kalla shekaru 25 a gidan yarin.

Alkaliyar ta kuma yanke wa korarren dan sandan hukuncin daurin rai da rai bisa kisa amma ba na ganganci ba.

Olalekan wanda da farko aka gurfanar da shi kan gisar gilla, amma kotun ta same shi da kisa ba da niyya ba.

Yayin shari'ar, masu binciken sun kira shaidu bakwai yayin da wadanda aka yi karar suka kira shaidu biyu.

Yayin shari'ar, wani likita Dr Oluwaseun Williams, ya bada shaida cewa, an harbi Johnson, dan shekara 35 sai shida.

Fashin Motar Dakko Kudi: A Yafe Min, Wannan Na Ne Farko, Korarren Jami'in DSS Ya Roki Alfarma

Kara karanta wannan

Donald Trump da ‘Ya ‘yansa 3 Za Su Bayyana a Kotu Bisa Zargin Tafka Sata a Amurka

A wani rahoton, Prosper Chijioke, korarren jami'in hukumar yan sandan farin kaya, DSS, da aka kama da hannu a fashin motar daukan kudi a Ntigha Junction a babban hanyar Enugu-Port Harcourt, yana roko a yafe masa, Vanguard ta rahoto.

Chijioke wanda aka yi holensa a hedkwatar yan sanda a Abia, Bende Road, tare da wasu mambobin tawagarsa 14 na yan fashi, ya yi ikirarin cewa wannan ne karon farko da ya aikata laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel