Fashin Motar Dakko Kudi: A Yafe Min, Wannan Na Ne Farko, Korarren Jami'in DSS Ya Roki Alfarma

Fashin Motar Dakko Kudi: A Yafe Min, Wannan Na Ne Farko, Korarren Jami'in DSS Ya Roki Alfarma

  • Tsohon jami'in hukumar DSS Prosper Chijioke da aka kama kan zargin yi wa motar dakko kudi fashi ya roki al'umma su yafe masa
  • Prosper ya ce kaninsa ne ya kawo gungun yan fashin gidansa suka raba kudi suka bashi wani kaso daga nan sai ya yanek shawarar shiga cikinsu
  • Yan sanda sun kama tsohon jami'in da wasu mutum tara ne kan zarginsu da tare motar dako kudi tare da kashe jami'in tsaro mai yi wa motar rakiya

Abia - Prosper Chijioke, korarren jami'in hukumar yan sandan farin kaya, DSS, da aka kama da hannu a fashin motar daukan kudi a Ntigha Junction a babban hanyar Enugu-Port Harcourt, yana roko a yafe masa, Vanguard ta rahoto.

Chijioke wanda aka yi holensa a hedkwatar yan sanda a Abia, Bende Road, tare da wasu mambobin tawagarsa 14 na yan fashi, ya yi ikirarin cewa wannan ne karon farko da ya aikata laifi.

Kara karanta wannan

Hotunan Wani Jami'in Sojan Bogi Da NSCDC Ta Kama a Nasarawa Yana Damfarar Mutane

Abia Taswira
Fashin Motar Kudi: A Yafe Min, Wannan Na Ne Farko, Korarren Jami'in DSS Ya Roki Alfarma. Hoto: @VanguardNGA
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin kora ta daga aiki - tsohon jami'in DSS, Prosper

Korarren jami'in na DSS, haifafan jihar Abia ya ce an kore shi ne daga aiki a shekarar 2007.

A kan dalilin korarsa daga aiki, ya ce ya tafi latti ne sabon wurin aikinsa bayan ya gama aiki a gidan gwamnati.

Ya ce:

"Lokacin da na gama aiki a gidan gwamnatin Abia, na dawo amma aka kore ni saboda na yi jinkirin fara aiki a sabon wurin da aka tura ni."

Da aka masa tambaya yadda ya fara aikata laifi, ya ce kaninsa ne ya kawo tawagar gida na kuma ya bashi wani kaso cikin kudin da suka samo.

Ya ce:

"Kani na ya kawo mambobin tawagar gida na kuma suka raba kudi suka bani wani kaso daga ciki."

Da aka masa tambayan dalilin da yasa ya karbi kudin duk da ya san na haram ne da hukuncin hakan, ya nemi bada hakuri ya nemi a yafe masa.

Kara karanta wannan

Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

A yafe min, wannan ne na farko kuma na yi alkawarin ba zan sake ba, Prosper

Ya ce wannan ne karo na farko da ya aikata laifi kuma ya rantse ba zai cigaba da irin wannan rayuwar ba.

"Na tambayi kani na kuma ya fada min yadda suka samo kudin. Ina son rokon al'umma su yafe min. Wasu daga cikin mu ba da gangan muka fada laifi ba.
"Ya faru amma muna son a yafe mana. Tabbas da hannu na saboda ba zan iya cewa banda ni ba kuma ban hana kani na raba kudin da ni ba. Wannan ne karon farko da na yi laifi."

Rahotanni sun ce gungun yan fashin sun sace N30 miliyan daga motar dakko kudin mallakar wata bankin zamani amma yan sanda sun gabatar da N10 miliyan da suka kwato daga hannunsu.

Makaman da aka kwato hannun wadanda ake zargin

An kuma kwato makamai da suka hada da Machine Gun, GPMG da AK-47 bakwai da harsasu a hannunsu.

Kara karanta wannan

Jama'a sun sha mamakin yadda wani dan Najeriya ke tikar aikin wahala a Dubai

An bindige daya cikinsu yayin musayar wuta da jami'an tsaro a fashin da ya yi sanadin mutuwar daya cikin jami'an da ke yi wa kudin rakiya, wasu yan sanda sun jikkata.

An Gano Miliyoyin Kuɗin da 'Yan Fashi Suka Sace a Motar Dakko Kudi a Gidan Tsohon DSS

Tunda farko, kun ji cewa tsohon jami'in hukumar DSS, Prosper Israel, da wasu mutum tara sun shiga hannu kan zargin hannu a fashin miliyoyin naira daga wata Mota mai dakon kudi tare da kashe mai rakiya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Da take nuna waɗanda ake zargi a Hedkwatar hukumar 'yan sanda dake Umuahia, babban birnin Abiya, jiya Litinin, kwamishinar yan sanda, Misis Jenet Agbede, tace an samu N10,184,000 a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel