Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

  • Yayinda Najeriya ke kukan rashin kudi kuma take shirin ciyo basussuka, farashin tushen arzikinta ya fadi
  • Najeriya na cigaba kukan ana saceta mata danyen mai kuma ba ta iya fitar da isasshen mai
  • Ministar kudi, Zainab Shamsuna, ta ce Najeriya za ta ciyo bashi a kasafin kudin 2023

Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya fadi a ranar Juma'a, 23 ga watan Satumba yayinda Najeriya ke fama da satar danyen mai dake gudana a kudancinta.

Bisa alkaluman da Legit ta gano a Business Insider, kawo karfe 2 na rana (agogon Najeriya da Nijar) Gangan Man Brent Crude ya fadi da 4.65% zuwa $85.48 yayinda Man Amurka ya fadi $80.64.

Wannan shine fadi mai muni da farashin mai zai yi cikin watanni tara da suka gabata.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Danyan
Najeriya Ta Shigesu: Farashin Danyen Man Ya Fadi A Kasuwar Duniya

Hakazalika rahoton MSCI ya nuna cewa a ranar Juma'a Dalar Amurka ta yi tsadar da bata taba yi ba cikin shekaru 20, rahoton TheCable.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da kari, Fam (£) na birtaniya ya yi irin faduwar da bai taba yi ba cikin shekaru 37 yayinda sabon ministan kudin Birtaniya, Kwasi Kwarteng, ya sanar da karban basussuka da yafewa mutane wasu kudaden haraji.

A ranar Laraba, Baitul Malin ajiyar kudin Amuka ya kara kudin ruwa da alkaluma 75 kuma hakan ya ingiza wasu kasashen duniya yin hakan, wanda ka iya haifar da matsin tattalin arziki.

Idan kuma aka samu matsin tattalin arziki zai shafi farashin mai, masana sun yi gargadi.

Ku Taimaka Ku Yafe Mana Basussukan Da Ake Binmu: Shugaba Buhari Ya Roki Shugabannin Duniya

A wani labarin kuwa, shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da shugabannin kasashen duniya su yafewa Najeriya da kasashe masu tasowa basussukan da suke binsu saboda halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano Ta Mayar Da Gidan Maitama Sule Cibiyar Demokradiyya

A jawabin da yayi a taron gangamin majalisar dinkin duniya ranar Laraba, Buhari yace kasashe masu tasowa na fuskantar kalubale da dama, cike har da rashin iya bisa basussuka.

Ya bukaci shugabannin duniya su taimaka su sanya baki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel