Donald Trump da ‘Ya ‘yansa 3 Za Su Bayyana a Kotu Bisa Zargin Tafka Sata a Amurka

Donald Trump da ‘Ya ‘yansa 3 Za Su Bayyana a Kotu Bisa Zargin Tafka Sata a Amurka

  • Letitia James tayi karar Donald Trump da iyalansa da wani babban jami’in kamfaninsa a kotun New York
  • Lauyar tana tuhumar tsohon shugaban kasar Amurkan da laifin yin da’awar ya mallaki tarin kudin da bai da su
  • James tace mutanen Trump sun yi ta ikirarin yana da dukiyar da ba gaskiya ba ne, saboda su kara azurta kansu

NEW YORK - Donald Trump da ‘ya ‘yansa uku, da abokin kasuwancinsa sun zama abin zargi a kasar Amurka bayan an shigar da wani kara gaban Alkali.

Reuters tace babban lauyar gwamnatin New York, Letitia James ta kai karar wadannan mutane a kotun jihar New York ta Manhattan a makon nan.

Letitia James ta fadawa kotu cewa an yi wa Duniya karya, inda aka yi shekaru ana zuzuta abin da Donald Trump ya mallaka, wanda aikata hakan laifi ne.

Kara karanta wannan

Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko

Lauyar take cewa Trump Organization sun boye gaskiyar dukiyar fitaccen ‘dan siyasar wajen fitar da takardun bayanan kudinsa na shekarun 2011-2021.

Trump ya amfana da karyar dukiya

A cewarta, Trump yana ikirarin ya mallaki dukiyar da bai da ita saboda ya shahara, kuma ya rika samun alfarma a banki, ya mori tsarin inshora mai tsoka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan kara da aka kai kotu mai tsawon shafuka 214 ta hada da ‘ya ‘yan tsohon shugaban kasar uku - Donald Trump Jr, Eric Trump, sai Ivanka Trump.

Donald Trump
Eric Trump, Donald Trump Jr, Ivanka Trump da Donald Trump a 2014 Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

Shi ma Allen Weisselberg wanda ya dade yana aiki a kamfanin attajirin zai kare kan shi a kotu.

Kakakin babban lauyan gwamnatin, Damian Williams ya ki cewa uffan da aka nemi ra’ayinsa a kan batun, wanda ba shi ne na farko a kan Trump ba.

Sharrin 'yan adawa ne - Trump

Kara karanta wannan

Jonathan: Abin Da Ya Sa Na Kira Buhari a Waya Kafin a Gama Kirga Kuri’un 2015

A wani rahoton da Reuters ta fitar, an ji cewa Mai girma Donald Trump ya yi magana a shafinsa na sada zumunta, yana mai musanya wannan zargi.

Trump mai shekara 76 da haihuwa yace wannan yana cikin taso shi gaba da ake yi tun da ya bar kujerar shugaban kasar Amurka a farkon shekarar 2021.

Lauyar tana shirin yin takara a New York, haka kuma ana tunain ‘dan siyasar zai sake neman takarar shugaban kasa a 2024 domin karasa wa’adinsa.

Charles III ya zama Sarki

A baya an ji labari babban ‘dan Queen Elizabeth II da Prince Philip ya dare karagar gidan sarautar Birtaniya, don haka ne muka tsakuro maku tarihinsa.

Sarki Charles III ya gaji mahafiyarsa wanda ta rasu bayan tayi shekaru 70 tana kan mulki a kasar Ingila. Shekara 70 aka yi ana jiran ranar da zai yi mulki.

Kara karanta wannan

Hauhawar Farashin Kaya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel