Miji Ya Tasa Matarsa a Gaba, Yana Mata Dariya Yayin da Take Girki da Gawaye a Madadin Gas

Miji Ya Tasa Matarsa a Gaba, Yana Mata Dariya Yayin da Take Girki da Gawaye a Madadin Gas

  • Wani dan Najeriya ya tasa matarsa a gaba yana mata dariya saboda yadda ta amince ta sauya daga girkin da gas zuwa gawayi
  • A cewar mijin, a baya matar ta ce ba za ta taba amfani da murhun gargajiya ba, amma dai yanzu ta ga yadda abubuwa suka kasance
  • Jama'a a kafar sada zumunta sun bayyana martaninsu, wasu sun ce ya kamata ya yi murnan samun mata ta gari

Wani dan Najeriya ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ya yin da ya yada bidiyon matarsa na girki da murhun gawayi.

A wani gajeren bidiyo da @ismailamzat01 ya yada a TikTok, an ga mutumin na kyalkyalewa da dariyar mugunta yayin da matar ke girki.

Yadda miji ya sa matarsa a gaba, yana mata dariya saboda tana girki da gawayi
Miji Ya Tasa Matarsa a Gaba, Yana Mata Dariya Yayin da Take Girki da Gawaye a Madadin Gas | Hoto: TikTok/@ismailamzat01
Asali: UGC

A cewar mutumin, yana dariya ne saboda akwai lokacin da ta dage cewa ba za ta taba amfani da murhin gawayi ba, amma gashi ta tsinci kanta a amfani dashi.

Matar dai bata ce komai a bidiyon ba, kawai ta mai da hankali ne ga abin da take yayin da mijin ke kwasar dariya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon:

'Yan TikTok sun yi martani ga bidiyon

'Yan TikTok sun ankarar da mutumin, sun ce ya daina dariyar mugunta, domin kuwa ya samu mata mai tausayi tunda ta iya fahimtar halin babu da kasar nan ke ciki.

Wasu suka ce ya fara kirga kansa cikin wadanda suka yi sa'a a rayuwa ba wai yai ta dariyar mugunta ba.

Ga dai abin da wasu ke cewa:

@yahayaabubakar605 yace:

"Ka yi matukar sa'a"

@A_s_Aliyu yace:

"Babu yanayin da mutum zai tabbata a ciki, rayuwa na sauyawa."

@tochiibe346 yace:

"Ya kamata ka godewa Allah ya ba da wacce ta dace."

@Abiodun 01 yace:

"Tattalin arzikin Najeriya ya sa ta zama matar kirki karfi da yaji."

Bidiyon Yadda Matashi Dan Najeriya Ya Cinye Malmala 10 Na Tuwo, Ya Ba da Mamaki

A wani labarin, wani dan Najeriya ya more, ya tafi gida da kyautar N10,000 bayan da cinye malmala 10 na tuwo da faranti daya na miya.

Ya cinye tuwon ne cikin kankanin lokaci, inda ya banke wani matashin da ya lamushe malmala 9 nan take duk dai a cikin mintuna 10.

A bidiyon mai ban dariya da @mariam_oyakhilome ta yada a TikTok, an ga matashin na hadiye lomar tuwo kamar mai jefa duwatsu a cikin rami.

Asali: Legit.ng

Online view pixel