Bidiyon Yadda Matashi Dan Najeriya Ya Cinye Malmala 10 Na Tuwo, Ya Ba da Mamaki

Bidiyon Yadda Matashi Dan Najeriya Ya Cinye Malmala 10 Na Tuwo, Ya Ba da Mamaki

  • Wani bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani dan Najeriya da ya iya cinye tulin tuwo cikin mintuna 10
  • Hakazalika, ya yi amfani ne da kwanon miya daya kacal, kuma ba tare da kari ba, lamarin da ya ba wasu mamaki
  • Wannan dai ya faru ne a wurin gasar cin abinci da aka yi a wani wuri, a gasar ya banke wani da ya iya cinye kunshi 9 na tuwo

Wani dan Najeriya ya more, ya tafi gida da kyautar N10,000 bayan da cinye malmala 10 na tuwo da faranti daya na miya.

Ya cinye tuwon ne cikin kankanin lokaci, inda ya banke wani matashin da ya lamushe malmala 9 nan take duk dai a cikin mintuna 10.

Kara karanta wannan

Jama'a sun sha mamakin yadda wani dan Najeriya ke tikar aikin wahala a Dubai

Yadda matashi ya cinye malmala 10 na tuwo
Bidiyon Yadda Matashi Dan Najeriya Ya Cinye Malmala 10 Na Tuwo, Ya Ba da Mamaki | Hoto: TikTok/@mariam_oyakhilome.
Asali: UGC

A bidiyon mai ban dariya da @mariam_oyakhilome ta yada a TikTok, an ga matashin na hadiye lomar tuwo kamar mai jefa duwatsu a cikin rami.

Abokin gasarsa shi ma ba tayar baya bane a iya lashe abinci, amma da cikinsa ya dauki caji da yawa, sai ya fara sarewa ta hanyar rage adadin saurin jefa lomomi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutane da dama ne suka mamaye filin gasar, kuma sun shiga mamakin yadda wadannan mutane masu matukar ci suka iya cinye tulin tuwo a mintuna 10.

A sadda ya kammala cinyewa, masoyansa sun yi ihu tare da bayyana alfaharin nasu ne ya cinye gasar.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@wisdomobinna817 yace:

"Ko da ma ban cinye ba, a je dai na ci rabo na.

@Caleb Oluwatimilehin yace:

"Ni dai sai kallon mutumin da ke sanye da shudiyar riga nake."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani bene ya ruguje a wata jihar Arewacin Najeriya

@debsan885 yace:

"Kashin mutumin nan dole ya yi tauri."

@Raph_Jayy yace:

"Na tabbata wannan mutumin ba zai yi kwanan lafiya ba yau."

@user86123649213388 yace:

"Zan koma gefe guda ne na yi amai abi na."

@qweku Yaro yace:

"Wannan wane irin tuwo ne haka? Ina magana ne a matsayina na dan Ghana."

@user5108369678359joy vera yace:

"Mutumin nan suma zai yi a waje."

@Ibuowo Kazeem yace:

"Na san wanda zai iya cinye malmala 16 na tuwo."

@ladyp yace:

"Na san yarinyar dake cinye malmala 10 cikin mintuna 6, ba tare da shan ruwa ba."

Wani Dan Najeriya Ya Fito Faifan Bidiyo, Ya Nuna Sana’ar da Yake Yi a Dubai

A wani labarin, cece-kucen jama'a ya mamaye wani bidiyon da aka yada a intanet na wani matashi dan Najeriya dake nuna sana'ar da yake a Najeriya.

Wannan lamari na matashi ya ba mutane da dama mamaki, ganin yadda birnin Dubai ya kai iyakar birni amma ake samun aiki irin wannan a madadin aiki mai gwabi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Bidiyon da aka gani a TikTok, mutumin da ba a san sunansa ba ya bayyana sana'ar da yake yi. Ya dai yi aikin ne a cikin bidiyon ba tare da furta kalma ko daya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel