Mutanen Kauye da Ke Shirin Tserewa Harin ’Yan Bindiga Sun Nutse a Kogi a Abuja

Mutanen Kauye da Ke Shirin Tserewa Harin ’Yan Bindiga Sun Nutse a Kogi a Abuja

  • Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki wani yankin babban birnin tarayya Abuja, mutane sun tsere a wani kauye
  • Akalla mutane biyar ne suka hallaka a wani kogi a lokacin da suke kokarin tserewa harin 'yan ta'addan
  • Babban birnin tarayya bai tsira daga yawaitar hare-haren 'yan ta'addan da suka addabi yankin Arewa ba

Abaji, Abuja - Mutum biyar; maza hudu da wata matar aure sun nuste a garin tserewa harin 'yan bindiga a kauyen Chakumi a unguwar Gurdi ta Abaji a Abuja.

Rahoton Daily Trust ya ce, Chakumi gari ne mai makwabtaka da kauyen Daku mai hade da kogin Gurara a unguwar Dobi ta Gwagwalada a birnin na Abuja.

Mai garin Chakumi, Mohammed Magaji ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce hakan ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.

Yadda mutum 5 suka mutu a garin gujewa harin 'yan bindiga a Abuja
Mutanen Kauye da Ke Shirin Tserewa Harin ’Yan Bindiga Sun Nutse a Kogi a Abuja | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Ya kuma ce, wadanda suka mutun, ciki har da matar aure mai kananan shekaru na aiki ne a gona lokacin da 'yan bindiga suka kai hari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce da ganin 'yan bindigan, sun gaggauta hawa kwale-kwale domin tserewa zuwa kauyen Dakuke, amma hakan ya zama sanadi suka rasa rayukansu a kogin na Gurara.

A cewarsa:

"Ko da yanzu da muke magana, ba a ciro gawarwakin mutanen da suka mutun ba saboda masunta daga Daku da kuma kauye na ci gaba da neman gawarwakin."

Magaji ya koka da yadda 'yan bindiga suka addabi yankin, ya kuma ce manoma sun daina zuwa gonakinsu saboda tsoron ta'addancin 'yan bindiga.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Abaji, Ibrahim Abubakar ya tabbatar da lamarin, ya kuma ce daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa dasu danginsa ne.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda, DSP Adeh Josephine bata amsa kiran waya ba, bata kuma dawo da sakon tes da majiya ta aike mata ba.

'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Banga, Sun Sace Mutane da Yawa a Neja

A wani labarin na daban, 'yan bindiga a jihar Neja sun kashe wani dan banga sun kuma raunata wani da harbin bindiga a yankin Ebbo ya karamar hukumar Lapai a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, an kuma yi awon gaba da wasu 'yan kauye da dama a yankin na jihar Neja.

An ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun farmaki Ebbo ne da misalin karfe 10:45 na dare, inda suka tafi kai tsaye ga ofishin 'yan bangan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel