Ba Zan Iya Tilastawa Ayu Ya Yu Murabus Ba, Atiku Ya Yi Martani Ga Sansanin Wike

Ba Zan Iya Tilastawa Ayu Ya Yu Murabus Ba, Atiku Ya Yi Martani Ga Sansanin Wike

  • Yayin da ake ci gaba da jayayya tsakanin 'yan tsagin Atiku Abubakar da Nyesom Wike a PDP, dan takarar shugaban kas aya yi bayani
  • Gwamna Wike da masu mara masa baya na son ganin an tsige shugaban PDP na kasa, Ayu saboda dalilai na siyasar yanki
  • Atiku ya ce sam bai da ikon tilastawa Ayu ya ajiye aikinsa, ya kuma bayyana dalilansa na fadin haka

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, ba zai iya tilastawa shugaban PDP Iyioricha Ayu ya ajiye mukaminsa na shugabancin jam'iyya ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a martaninsa ga 'yan tsagin gwamnan Ribas Wike da ke ta kira ga tube Ayu a matsayin shugaban PDP na kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Atiku ya yi bayani game da kiran tsige shugaban PDP
Ba Zan Iya Tilastawa Ayu Ya Yu Murabus Ba, Atiku Ya Yi Martani Ga Sansanin Wike | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tun bayan kammala zaben fidda gwanin PDP da ya kawo Atiku a matsayin dan takarar shugaban da kuma zabo gwamna Okowa a matsayiin abokin takarar Atiku ake kai ruwa rana da Wike.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Jiga-jigan 'yan siyasan da ke kusa da Wike sun dage cewa, bai kamata a samu dan takarar shugaban kasa daga Arewa ba, kana shugaban jam'iyya ma daga yankin ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata ganawar da suka yi a gidan Wike, sun tattauna matsayarsu, inda suka ce tabbas dole ne Ayu ya sauka a daura wani kafin su goyi bayan Atiku.

A bangare guda, ya ce duk wasu matsalolin PDP za su karshe, inda ya nemi 'yan jam'iyyar su hada kai domin ciyar da kasa gaba.

Jam'iyyar PDP na cikin rudani tun bayan da Atiku ya zabi gwamnan Delta a matsayin abokin takara.

INEC Ta Manna Sunan Shekarau a Matsayin Dan Takarar Sanatan NNPP, Duk da Sauya Sheka Zuwa PDP

A wani labarin na daban kuma, bayan kammala wani zama a yau Talata 20 ga watan Satumba, hukumar zabe mai kanta (INEC) ta fitar da sunayen 'yan takarar da za su gwabza a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin ASUU da majalisa, za a kai batu gaban Buhari kafin a koma makaranta

Jerin da INEC ya fitar na dauke da sunaye, jam'iyyu, matakin karatu da shekarun kowane dan takara, TheCable ta ruwaito.

An bayyana bayanan dukkan 'yan takara, amma a bangaren jihar Kano, an samu tsaiko ko kuskuren wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel