Mata Sun Yi Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Hijabi, Sun Kone Lullubi a Kasar Iran

Mata Sun Yi Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Hijabi, Sun Kone Lullubi a Kasar Iran

  • Rikicin zanga-zanga ya barke a Iran tun bayan mutuwar wata mata da aka tsare saboda saba dokar sanya Hijabi
  • Mata sun fito titi suna ta kone Hijabi domin nuna fushinsu ga abin da ya faru da matar mai shekaru 22
  • Kasar Iran na daya daga cikin kasashen muslunci a duniya, kuma akwai dokoki masu tsauri kan sanya Hijabi

Sari, Iran - Zanga-zangar mata a kasar Iran na kara kamari biyo bayan mutuwar wata mata da aka tsare a magarkama bisa zargin saba dokar sanya Hijabi, rahoton Al-Arabiyya.

Mata sun yi tururuwa a kasar, inda suka kone Hijabai da don nuna fushi da kun jinin abin da ya faru a yankin Sari a jiya Talata, rana ta biyar kenan bayan fara rikicin.

Kara karanta wannan

Kisan Ummita: An Gurfanar da ‘Dan Chana, Kotu ta Yanke Hukuncin Farko

'Yan gwagwarmayar matar na daya daga cikin uku da jami'an tsaro suka harbe a Urmia, Piranshahr da Kermanshah.

Tashin hankali a Iran, mata na zanga-zangar kin jinin hijabi
Mata sun yi zanga-zangar nuna kin jinin Hijabi, sun kone lullubi a kasar Iran | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sai dai, a bangaren hukumomin tsar, sun zargi masu zanga-zangar sun kashe mutum biyu Kermanshah da kuma jami'in dan sanda a Shiraz.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

At least seven people are now reported to have been killed since protests against the Hijab laws and morality police erupted after Mahsa Amini's death.

Ya zuwa yanzu, an ce akalla mutum bakwai ne aka kashe tun farin wannan zanga-zanga ta nuna kin jinin Hijabi da koka zalunci 'yan sanda da ta barke bayan mutuwar Mahsa Amini.

Wani bidiyo da muka gani a Twitter ya nuna lokacin da matan ke kone-kone da wake-wake da raye-raye a kan titi a Sari.

Kalli bidiyon:

Yadda lamarin ya faro

An tsawo tsaiko a lokacin da wata mata mai shekaru 22 daga birnin Saqez da ke Arewa maso Yammacin kasar ta mutu a asibiti ranar Juma'a, bayan ta shafe kwanaki uku a sume.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Rahoton BBC ya ce, matar dai Bakurdiya ce, kuma tana zaune da dan uwanta a Tehran ta Iran a lokacin da 'yan sanda suka kama ta.

An zarge ta da saba dokar sanya Hijabi, kamar yadda kasar ta tana. Ana bukatar mace ta sanya Hijabi, ko dan kwali, akalla dai ya zama ta rufe jikinta ruf.

An ce ta yanki jiki ta fadi jim kadan bayan kame ta, lamarin da daga baya ya kai ga mutuwar a lokacin da take hannun jami'an tsaro.

An kuma yada rahotannin da ke cewa, 'yan sanda sun yiwa Amini duka a ka, a cewar mukaddashin kwamishinan kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniya, Nada al-Nashid.

Sai dai, 'yan sanda sun karyata batun duka, sun ce kawai ta samu bugun zuciya ne nan take. Iyalanta kuwa sun ce lafiyarta kalau.

Kyakkyawan Karshe: Malamar Makaranta Ta Mutu Tana Tsaka Da Karatun Al-Qur'ani

A wani labarin, bidiyon wata malamar makaranta yar kasar Indonesia wacce ta rasu tana karatun Al-Qur'ani mai girma ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta na yanar gizo.

Kara karanta wannan

Mabaraci Ya Tsallake Rijiya Da Baya Yayinda Aka Kamashi Kudi N500,000 a jihar Legas

Bidiyon da aka dauka yayin wani taron addinin Musulunci ya nuna yadda Malamar ke karanta Suratul Baqara.

Bidiyon mai tsawon minti 1:29 ya nuna yadda ta fadi tana tsaka da karatun ta 163 na Suratul Baqarah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel