Majalisa ga DSS, 'Yan Sanda: Dole ne a Damko Maharan Tawagar Sanata Ubah

Majalisa ga DSS, 'Yan Sanda: Dole ne a Damko Maharan Tawagar Sanata Ubah

  • Majalisar dattawan Najeriya tayi Allah wadai da harin da 'yan bindiga suka kai kan tawagar Sanata Ifeanyi Ubah a jihar Anambra
  • Bata tsaya nan ba. ta yi umarni ga jami'an DSS, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su zakulo maharan cikin gaggawa
  • 'Yan majalisar sun mika godiya ga Ubangiji da Sanatan bai rasa ransa ba inda suka ce abun ya matukar girgiza zu

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta umarci rundunar ‘yan sandan Najeriya, jami'an tsaron farin kaya naDSS, da sauran hukumomin tsaro da zakulo ‘yan bindigar da suka kai wa ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah hari a Anambra.

Wannan umarni na daya daga cikin kudurorin da ‘yan majalisar suka bayyana a ranar Talata a zauren majalisar dokokin kasar da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin ASUU da majalisa, za a kai batu gaban Buhari kafin a koma makaranta

Majalisa
Majalisa ga DSS, 'Yan Sanda: Dole ne a Damko Maharan Tawagar Sanata Ubah. Hoto daga channesltv.com
Asali: UGC

Bayan hutun makonni ne ‘yan majalisar suka koma zaman majalisar a daidai lokacin da ake cigaba da gyaran zauren majalisar.

Sanata Uche Ekwunife yagabatar da bukatar neman izinin majalisar dattawa domin gabatar da wani lamari mai muhimmanci ga al’umma kan harin da aka kashe hadiman Ubah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martanin ‘yan majalisar, sun yi Allah wadai da lamarin, tare da bukatar jami’an tsaro da su gudanar da cikakken bincike kan harin da nufin kamawa tare da hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Sun kara da yanke shawarar yin shiru na minti daya domin girmama wadanda harin ya rutsa da su, tare da umartar hukumomin tsaro su mika rahoton bincikensu ga kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin tsaro da leken asiri, da kuma kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ‘yan sanda cikin makonni biyu.

“Lokacin da muka ji, mun dauka abin wasa ne domin ba za mu iya tunanin da rana tsaka irin wannan bala’in zai iya faruwa ba."

Kara karanta wannan

Babu Tabbacin Ahmad Lawan Zai Dawo Majalisa, Zai Rasa Takarar Farko Tun 1999

- Cewar Sanata Biodun Olujimi yayin da yake Allah-wadai da harin.

“Har yanzu dole ne mu kara yin abubuwa da yawa saboda wannan ya faru da rana ga mutumin da ke da ayarin motoci sama da shida, za ku iya tunanin abin da zai iya faruwa ga mutumin da ke tuka mota daya.
"Dole ne mu san masu aikata irin wadannan munanan al'amura a kasarmu. Ina mika ta’aziyyata ga Sanata Ifeanyi Ubah, kuma ina addu’ar Allah ya sawwake.”

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda bai ji dadin faruwar lamarin ba, ya yabawa Sanata Ekwunife da ya ja hankalin ‘yan majalisar kan lamarin.

“Duk abin da lamarin ya yi muni, dole ne mu gode wa Allah saboda rayuwar 'dan uwanmu da abokin aikinmu da ta tsira. Mun gode wa Allah da ya cece shi."

- Omo-Agege yace.

Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6

Kara karanta wannan

Cefanar da NNPCL: 'Yan Najeriya ba Zasu Fuskanci Wuyar Man Fetur ba a Watan Disamba

A wani labari na daban, 'yan Bindiga sun budewa tawagar motocin Sanata Ifeanyi Ubah wuta a garin Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka dake jihar Anambra ranar Lahadi.

Bidiyon da aka dauka bayan harin ya nuna cewa ana hasashen kimanin yan sandan shida aka kashe a musayar wutar, rahoton SaharaReporters.

Asali: Legit.ng

Online view pixel