Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6

Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6

Yan Bindiga sun budewa tawagar motocin Sanata Ifeanyi Ubah wuta a garin Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka dake jihar Anambra ranar Lahadi.

Bidiyon da aka dauka bayan harin ya nuna cewa ana hasashen kimanin yan sandan shida aka kashe a musayar wutar, rahoton SaharaReporters.

Wata majiya a riwayar Punch ta bayyana cewa:

"Wasu bata gari sun kaiwa Sanata Ifenyi Ubah hari a Enugwu Ukwu. Wannan shiryayyen hari ne. Kwantan bauna sukayi masa."
Ifeanyi
Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6
Asali: UGC

A cewar masu idanuwan shaida, wasu yan batagari ne suka budewa mototcin Sanatan wuta ba zato ba tsammani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga gawawwakin wasu hadimansa a kasa.

Kara karanta wannan

Adamawa: An biyashi N5000 da kwanon Shinkafa 4 don yayi kisan kai, ya kashe mutum 1, ya bar daya na jinya

An ce Sanatan ya tsallake rijiya da baya ne saboda motarsa ba ta jin harin bindiga, rahoton ChannelsTV.

Kakakin hukumar yan sandan jihar DSP Tochukwu Ikenga, ya bayyana cewa Kwamishanan yan sandna jihar tuni ya garzaya wajen don ganewa idonsa.

A jawabin da ya fitar da daren Lahadi, Ikenga ya bayyana cewa har yanzu dai ana tattara bayanai kan lamarin .

Daya daga cikin hadiman Sanatan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa an yi niyyar kashe Sanatan ne amma motar "Bulletproof ce".

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel