Cefanar da NNPCL: 'Yan Najeriya ba Zasu Fuskanci Wuyar Man Fetur ba a Watan Disamba

Cefanar da NNPCL: 'Yan Najeriya ba Zasu Fuskanci Wuyar Man Fetur ba a Watan Disamba

  • Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya tabbatar da cewa ba za a yi fama da matsalara karancin man fetur a watan Disamba ba
  • Kamar yadda jami'in kula da harkokin kudi na matatar, Umar Ajia, yace sun shirya tsaf domin samar da man fetur har zabe mai zuwa
  • Ya koka da yadda hatta kasashe masu makwabtaka da Najeriya ke morar ganimar tallafin man fetur saboda yanayin iyakokin kasar nan

Kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), ya ce kasar ba za ta fuskanci karancin man fetur ba a watan Disamba da kuma bayanta, saboda ta yi isassun shirye-shirye na samar da mai.

Babban jami’in kula da harkokin kudi na matatar, Umar Ajia, ya bayyana hakan a Abuja jiya a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar wakilai kan tsarin tallafin man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta haramtawa 'yan Najeriya cin gandan fatar dabbobi, ta fadi dalilai

Ajia ya ce, kamfanin ya shirya wasu isassun matakan dakile matsalar karancin man fetur a kasar baki daya ko bayan babban zaben shekarar 2023 mai gabatowa, The Nation ta rahoto.

NNPCL
Cefanar da NNPCL: 'Yan Najeriya ba Zasu Fuskanci Wuyar Man Fetur ba a Watan Disamba. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC
“Mun tsawaita kwangilar DSDP na watanni shida, don ci gaba da samar da PMS a fadin ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Kwangilar DSDP a gaskiya ta ƙare a watan Agusta kuma lokaci ne mai hatsarin gaske don fara sake sayar da shi saboda muna fuskantar lokacin hunturu, waɗannan su ne "watannin ember" masu wahala waɗanda muka saba guje wa karancin man fetur a cikinsu.
“Kun san cewa karancin da ake fama da shi a Najeriya yana da nasaba da lokacin Kirsimeti, don haka idan har yanzu kun amince, za a dauki wata daya ko biyu aikin.
“Don haka abin da hukumar ta amince da shi, shi ne a tsawaita kwangilar na tsawon watanni shida, ta yadda mun wuce damuna kuma mun yi zabe, idan ba haka ba za mu iya samun matsala a lokacin zaben.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam Ya Fashe a Babban Birnin Jihar Arewacin Najeriya

- Ajia yace.

Shugaban Kwamitin, 'dan majalisa Ibrahim Al-Mustapha (APC-Sokoto), ya ce akwai bukatar a sake duba farashin man fetur, daidai da farashin da ake samu a duniya.

Ajia ya ce, a sakamakon lalacewar iyakokin kasar nan, tallafin man fetur da ‘yan Najeriya za su sha ya kan kai har Mali da sauran kasashe makwabtan Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, Al-Mustapha ya ce ana sayar da man fetur a kan N536 a kowacce lita a jamhuriyar Nijar, N577 a Mali da kuma N389 a Jamhuriyar Benin.

“Idan kuna da N5 miliyan, za ku iya tsallaka kan iyaka da manyan motoci dankare da man fetur, kuma wannan ita ce gundarin gaskiya, iyakokinmu a bude suka; eh muna da kwastam amma ban san ya ake ba.”

- Yace

Kwamitin ya shiga wani taron sirri don ci gaba da tattaunawa kan lamarin.

Ambaliyar Ruwa: Mutum 92 Sun Rasa Rayukansu Yayin da Gwamna Ya Lula Yawon Shakawata Ketare

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

A wani labari na daban, yawan wadanda ambaliyar ruwa yayi ajali a jihar Jigawa ya haura inda ya kai har mutum 92.

Wannan yana zuwa ne yayin da Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, yake shan caccaka sakamakon shillawa kasar waje da yayi hutu ba tare da ziyartar wadanda ibtila'in ya fadawa ba.

yadda mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Lawan Adam, ya tabbatar da cewa mutum 92 suka rasa rayukansu tsakanin watan Augusta zuwa Satumba sakamakon ambaliyar ruwan, Premium Times ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel