Majalisar Wakilai Za Ta Gana da Buhari Bayan Cimma Matsaya da ASUU

Majalisar Wakilai Za Ta Gana da Buhari Bayan Cimma Matsaya da ASUU

  • Bayan cimma matsayar da za ta kai a dawo karatu, shugaban majalisa ya bayyana makomar zamansu da ASUU
  • Malaman jami'a a Najeriya na yajin aiki, akalla watanni 6 aka shafe dalibai na zaman banza a kasar
  • An samu cece-kuce bayan da hotuna suka yadu a kafar sada zumunta na yadda surukar Buhari ta kammala digiri a kasar waje

FCT, Abuja - Shugaban majalisar wakilai ta ce za ta gana shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i (ASUU), TheCable ta ruwaito.

Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a jiya Talata 20 ga watan Satumba awanni kadan bayan ganawar sirri da shugabannin ASUU da karamin ministan ilimi, Goodluck Opiah a majalisar dokokin kasar.

Majalisa ta gana da ASUU, za ta gana da Buhari idan ya dawo daga turai
Majalisar Wakilai Za Ta Gana da Buhari Bayan Cimma Matsaya da ASUU | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Ya ce da zarar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo, tabbas za su zauna dashi don tattauna sakamakon ganawar dashi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Surukar Shugaban Kasa, Zahra Bayero Ta Kammala Karatu Da Digiri Mafi Daraja

Idan baku manta ba, shugaba Buhari ya shilla birnin News York a Amurka domin halartar taro na 77 na majalisar dinkin duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bangare guda, 'yan majalisar sun kuma gayyaci akanta janar na kasa, hukumar NITDA, babban oditan kasa da kuma hukumar kula da albashi da kudaden shigan ma'aikata ta NSIWC don kammala zama da ASUU.

Hukumomi da kusoshin gwamnatin da aka gayyata za su bayyana a gaban majalisa a ranar Alhamis 22 ga watan Satumba.

Da yake magana bayan ganawarsa da ASUU, kakakin majalisa Gbajabiamila ya ce tabbas an samu wata 'yar mafita tsakaninsu da ASUU.

A cewarsa:

"Akwai abubuwa bakwai da ASUU ta gabatar - abin da muke ganin ya zama dole kafin su koma aji.
“Mun duba wadannan abubuwan guda bakwai kuma mun amince da wasu daga ciki ko dai kadan daga ciki."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta haramtawa 'yan Najeriya cin gandan fatar dabbobi, ta fadi dalilai

Martanin ASUU

A nasa martanin, shugaban ASUU Emmanuek Osodeke ya ce batutuwan da aka zanta da 'yan majalisar za a baje su a faifan mambobin kungiyar don tattaunawa, rahoton BusinessDay.

A kalamansa:

"Anan gaba kadan, batun (yajin aiki) zai warware."

Idan baku manta ba, kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta shiga yajin aiki tun ranar 14 ga watan Satumba saboda rashin samun wasu bukatu daga hannun gwamnati.

Da yawan dalibai na zaman banza a Najeriya, face kadan da suke shilla kasashen waje karatu ko suke karatu a jami'o'i masu zaman kansu a kasar.

Surukar Shugaban Kasa, Zahra Bayero Ta Kammala Karatu Da Digiri Mafi Daraja

A wani labarin, surukar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Nasiru Bayero, ta kammala karatunta na digiri.

Zahra, wacce ta kasance diya ga sarkin Bichi da ke jihar Kano, Alhajin Nasiru Ado Bayero ta kammala karatunta ne a fannin kimiyyar Gine-gine da digiri mafi daraja.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Surukarta kuma uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta je shafinta na Instagram don taya matar dan nata murnar wannan nasara da ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel