Amarya Ta Saka Kawayenta 100 A Dandalin WhatsApp, Ta Dorawa Kowannensu Harajin N5k Na Shagalin Bikinta

Amarya Ta Saka Kawayenta 100 A Dandalin WhatsApp, Ta Dorawa Kowannensu Harajin N5k Na Shagalin Bikinta

  • Wata mai shirin zama amarya ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya bayan ta bukaci kawayenta sun hada kudi don shagalin aurenta
  • A wata hirar WhatsApp da aka wallafa a Twitter, amaryar ta bukaci kawayenta kimanin su 100 su biya N5k kowannensu a matsayin gudunmawar bikinta
  • Jama’a sun yi martani ga sakonnin nata na WhatsAPP inda kowa ya bayyana ra’ayinsa

Wata mai shirin zama amarya ta nemi gudunmawar kudi daga wajen kawayenta kimanin su 100 gabannin bikin aurenta.

Matashiyar ta saka kawayen nata a wani shafi kan WhatsAPP sannan ta wajabta masu biyan akalla N5k kowannensu don bikinta.

Budurwa da kudi
Amarya Ta Saka Kawayenta 100 A Dandalin WhatsApp, Ta Dorawa Kowannensu Harajin N5k Na Shagalin Bikinta Hoto: Coffee and Milk / Maksym Kapliuk
Asali: Getty Images

Yusuf Bolaji wacce ta fallasa hirar a kan Twitter ta bayyana cewa N5k da kowannensu zai na daban ne baya ga sauran kudade da za a kashe da kuma biya.

Bolaji ta rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wata kawata da muka yi NYSC tare za ta yi aure a wata mai zuwa kuma ta saka kimanin mu sama da 100 a wani shafi sannan ta bukaci mu hada N5k kowannenmu don bikinta. 5k ba ma na anko ba fa Pekelepekele.”

Jama’a sun yi martani

Muhammad Karamba ya ce:

“Wannan ne dalilin da yasa naki shiga kowani dandalin aure na WhatsAoo. Hatta ga na aminina. Bana son matsin lamba mara tushe. Na san menene matsayinka a wajena kuma na san abun da zan iya bayarwa.”

B Energy ta yi martani:

“Abu ne mai kyau amma ba ita za ta kayyade nawa za a hada mat aba, kuma bai kamata ta tilastawa kowa ba.”

Jelilat Ibrahim ta kara da cewa:

“Kala-kala. Hakan bai yi dadi ba! Abun dariya shine mutanen da suka hada kudin sune za su fito su fada, ba mu bane muka hada kudin da tayi auren da shi.”

Kalli wallafar a kasa:

Zan Saketa Bayan Wata 2 Sai Muyi Aurenmu: Matashi Ya Sanar Da Budurwarsa Labarin Aurensa Da Wata Daban

A wani labarin, wata matashiyar budurwa ta shiga halin damuwa bayan samun labarin auren saurayinta da suke soyayya da juna.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter, budurwar mai suna Salma ta bayyana yadda saurayin da take matukar kauna ya sanar da ita batun aurensa da wata daban.

Ko da ya sanar da Salma cewa ya yi aure da fari bata yadda ba don duk a zatonta zolayarta yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel