Zan Saketa Bayan Wata 2 Sai Muyi Aurenmu: Matashi Ya Sanar Da Budurwarsa Labarin Aurensa Da Wata Daban

Zan Saketa Bayan Wata 2 Sai Muyi Aurenmu: Matashi Ya Sanar Da Budurwarsa Labarin Aurensa Da Wata Daban

  • Wata matashiyar budurwa ta ba da labarin yadda abubuwa suka wakana tsakaninta da masoyinta wanda ya auri wata ba tare da saninta ba
  • Budurwar mai suna Salma tana tsananin son saurayin nata kuma bata yi tsammanin haka daga gare shi ba
  • Sai dai saurayin ya nuna ita matar da ya aura zabin mahaifiyarsa domin kuwa suna da dangantaka da ita

Wata matashiyar budurwa ta shiga halin damuwa bayan samun labarin auren saurayinta da suke soyayya da juna.

A wata wallafa da tayi a shafinta na Twitter, budurwar mai suna Salma ta bayyana yadda saurayin da take matukar kauna ya sanar da ita batun aurensa da wata daban.

Budurwa da sako
Na Rasa Inda Zan Sa Kaina: Budurwa Ta Ba Da Labarin Yadda Saurayinta Ya Auri Wata Ba Ita Ba Hoto: @salmerrhhh / Halfpoint images
Asali: Twitter

Ko da ya sanar da Salma cewa ya yi aure da fari bata yadda ba don duk a zatonta zolayarta yake yi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yadda Matar Aure Ta Mutu A Hatsarin Mota Yayin Kokarin Kama 'Budurwar' Mijinta

Sai dai kuma, duk da auren da yayi, saurayin ya nuna mata kamar shi ba son auren yake yi ba duk hadi ne na mahaifiyarsa sannan ya roketa da ta yafe masa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ya sha alwashin sakin amaryar da zaran sun yi watanni biyu tare sannan ya yi alkawarin aurenta a farkon shekara mai zuwa.

A takaice budurwar tayi masa fatan alkhairi a gidan aurensa sannan ta toshe lambarsa ta yadda ba zai kara iya aike mata da sako ba.

Da take wallafa hotunan hirar tasu a soshiyal midiya, Salma tace bata san yaya za tayi da wannan radadi da take ji a zuciyarta ba.

Ta ce:

“Zuciyata tayi nauyi yanzu haka. Ban san ta yaya zan tsallake wannan abun ba.”

Kalli wallafar tata a kasa:

Bidiyo: Hirar Karshe Da Budurwar Da Dan China Ya Kashe Tayi Da Kawarta, Ya Kasance Akan Mutuwa

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Yar Najeriya Mazauniyar UK Ta Fatattaki Mijinta Daga Gida Saboda Ya Kira Mata Yan Sanda

A wani labarin, mun ji cewa Al’ummar unguwar Janbulo dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano suka wayi gari da wani mummunan al’amari na kisan wata matashiya mai suna Ummita.

Wani mutumin kasar China ne ya bi budurwar mai shekaru 23 har cikin dakinta da ke gidan iyayenta sannan ya yanka ta da wuka.

A daidai lokacin da jama’a ke jimamin wannan al’amari sai ga wani bidiyo na hirar da marigayiyar tayi da wata kawarta mai suna Sarauniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel