Wasu Samari Biyu Sun Ba Hammata Iska Kan Budurwa a Nasarawa, An Illata Ɗaya

Wasu Samari Biyu Sun Ba Hammata Iska Kan Budurwa a Nasarawa, An Illata Ɗaya

  • Wasu matasa biyu sun kaure da faɗa kan budurwa mai suna Aisha a jihar Nasarawa, an cire wa ɗaya hannu
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, yace sun kai wanda ya jikkata Asibiti kuma sun kama wanda ake zargi
  • Bayanai sun nuna cewa lamarin ya fara ne kan saɓanin da ya shiga tsakaninsu kan Aisha, ɗaya ya zare makami

Nasarawa - Wani matashi mai suna Jibril Abdullahi ɗan shekara 25 a duniya ya tsinci kanshi cikin yanayin baƙin ciki yayin da ya rasa hannunsa ɗaya wurin faɗa kan budurwa a jihar Nasarawa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani saurayi mai suna, Usman Ɗanladi, ya farmaki Jibril Abdullahi bisa zargin yana soyayya da budurwarsa.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, yace tuni suka kama Ɗanladi bisa zargin yunƙurin kisan kai.

Dakarun hukumar yan sanda.
Wasu Samari Biyu Sun Ba Hammata Iska Kan Budurwa a Nasarawa, An Illata Ɗaya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa, sun samu bayani ranar 16 ga watan Satumba, 2022 da karfe 4:00 na yamma cewa an farmaki Jibrin Abdullahi, mazaunin Tudun Wada, Auta Balefi dake yankin ƙaramar hukumar Karu, kuma an tsire masa hannu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

DSP Nansel yace nan take jami'an yan sanda na Caji Ofis ɗin Goshen City bisa jagorancin CSP Eunice Ogbadu, suka kai ɗauki wurin kuma suka yi saurin kai mutumin Asibitin FMC Keffi don kula da lafiyarsa.

Kakakin yan sandan yace:

"Da aka tsananta bincike don gano wanda ya aikata wannan ɗanyen aiki sakamako ya yi kyau a ranar 17 ga watan Satumba lokacin da wanda ake zargi na farko, Usman Ɗanladi, da ake kira 'Makashi' ya shiga hannu."

Meyasa ya aikata masa wannan ɗanyen aiki?

DSP Nansel ya yi bayanin cewa da aka tuhumi wanda ake zargin ya amsa laifin amma ya yi ikirarin cewa tun farko Abdullahi ya ci mutuncin budurwarsa mai suna Aisha.

Kakakin yan sandan yace wanda ake zargin ya gaya musu yayin da ya fuskanci matashin kan abinda ya yi wa Aisha sai faɗa ya kaure tsakaninsu, garin haka ne ya kai masa sara da Adda.

A halin yanzu, kwamishinan yan sandan Nasarawa, CP Adesina Soyemi, ya umarci a maida Kes ɗin sashin binciken manyan laifuka dake Lafiya, don tsananta bincike.

Ya ƙara da cewa zasu miƙa lamarin hannun Kotu domin hukunta wanda ake zargi da zaran sun kammala bincike, kamar yadda PM News ta ruwaito.

A wani labarin kuma Malam Aminu Daurawa ya bayyana shawarwarin da ya ba Ummita kafin saurayinta ɗan China ya halakata a Kano

Shehin malamin nan Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayanin wayar da ya yi da Marigayiya Ummakulsum Buhari wanda wani ‘dan kasar Sin ya kashe.

Babban malamin yake cewa wannan Baiwar Allah da aka sani da Ummita ta fada masa cewa iyayenta sun hana ta auren wannan saurayi da ya zo daga Sin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel