Yadda Matar Aure Ta Mutu A Hatsarin Mota Yayin Kokarin Kama 'Budurwar' Mijinta

Yadda Matar Aure Ta Mutu A Hatsarin Mota Yayin Kokarin Kama 'Budurwar' Mijinta

  • Wata matar aure ta riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ta yi yayin da ta ke kokarin kama mijinta da 'budurwarsa' a Calabar
  • Rahotanni sun bayyana cewa matar ta isa wani kanti ne sai ta hangi mijinta yana fitowa daga kantin tare da wata mace da ake zargin budurwarsa ne
  • Bayan matar ta gaza hana dakatar da mijin da matar barin kantin a cikin mota, ta bi bayansu a motarta amma ta yi hatsari saboda gudu fiye da kima da ta ke yi

Calabar - Kwamanda Hukumar Kiyayye Haddura na Kasa, FRSC, na Jihar Cross Rivers, Maikano Hassan, ya tabbatar da cewa hatsari ya kashe wata mata mai matsakaicin shekaru a Calabar, ranar Lahadi yayin da ta ke bin 'budurwar' mijinta a mota.

Kwamandan wanda ya yi magana da jaridar Vanguard a daren ranar Lahadi, ya ce zura gudu fiye da kima da matar ke yi na ya janyo hadarin.

Mota Toyota
Yadda Motar Aure Ta Mutu A Hatsarin Mota Yayin Kokarin Kama 'Budurwar' Mijinta. Hoto: @VanguardNGA
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce hatsarin ya da ritsa da mota kirar Toyota Highlander da ya faru a babban titin Muritala Mohammed a Calabar ya yi sanadin mutuwar matar da ita kadai ke tuka motar.

Kalamansa:

"Duk da cewa an garzaya da mtar asibiti mafi kusa, an ce ta rasu bayan yan mintuna saboda rauni da ta samu sakamakon hatsarin."

Vanguard ta tattaro cewa matar tana zura gudu ne tana bin mijinta wanda aka ce yana tare da wata mata da ake zargin 'budurwarsa' ne amma motar ya kwace mata, kuma hakan ya yi sanadin mutuwar ta.

Wata majiya wacce bata son a ambace ta ta shaidawa Vanguard cewa matar ta hangi mijinta yana fitowa dafa kantin SPAR tare da wara mace kuma ta yi kokarin tare motar mijinta da motarta kirar Toyota Highlander.

Majiyar ta ce:

"Mijinta, shi kuma ya yi kokari ya kaucewa motarta sannan ya bi babban hanya Murtala Muhammed, sannan matar ta bi shi a guje da motarta.
"A kokarin ta na cimma mijinta, motar ta kwace mata, ta kwace daga titi ta yi karo da wata bishiya, ta lalata motar ta yadda ba zai gyaru ba kuma ta kashe kanta."

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

A wani labarin, jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel