A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

  • Wani magidanci ya halaka matarsa saboda ta tambaye shi ya biya ta bashin N1000 da ya karba
  • Rahotanni sun bayyana cewa magidancin mai shekaru 41 ya buga kan matarsa da bango ne kuma ta suma
  • Yan uwan matar mai suna Rabiyatu Usman sun garzaya caji ofis sun yi wa yan sanda korafi kuma nan take aka kama mijin

Jami'an yan sanda na jihar Adamawa sun kama wani mutum mai shekaru 41, Usman Hammawa, bisa zarginsa da yi wa matarsa mai shekaru 36 duka, saboda N1,000 har sai da ta mutu.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin Rabiyatu Usman da mijinta ne bayan ta bukaci ya biya ta bashin N1,000 da ya karba daga hannunta.

Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Duka a Adamawa Saboda N1000
Taswirar jihar Adamawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Usman Hammawa, mazaunin yankin Jada a karamar hukumar Ganye ta jihar Adamawa, ya halaka matarsa ne ta hanyar buga kanta da bango, hakan yasa ta fadi sumammiya.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Hatsarin mota ya hallaka mutane da dama a hanyar zuwa Minna

Kamar yadda rahoton na Daily Trust ya ce, an garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar ta riga mu gidan gaskiya.

'Yan uwan matar suka yi korafi wurin yan sanda

Yan sanda sun kama wanda ake zargin bayan yan uwan matar sun shigar da korafi a ofishin yan sanda da ke karamar hukumar Ganye.

Usman, wanda ma'aikacin gwamnati ne a karamar hukumar Ganye, yana da yara biyar tare da marigayiyar bayan shekaru 16 da aure.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Nguroje, ya ce kwamishinan yan sandan jihar, CP Aliyu Adamu Alhaji, ya yabawa mazauna garin da yan sanda bisa tona asirin wanda ya aikata laifin domin ya girbi abin da ya shuka.

Amma, ya bada umurnin a gudanar da bincike ba tare da hayaniya ba domin a tabbatar wanda ake zargin ya fuskanci sakamakon laifinsa.

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

A wani labarin daban, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel