Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

  • Hamza Al-Mustapha, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Action Alliance, AA, ya karbi bakuncin kungiyoyin mata kirista a gidansa
  • Yayin tattaunawa da ya yi da matar kan batutuwan da ke faruwa a Najeriya, tsohon babban dogarin na marigayi Sani Abacha ya zubar da hawaye
  • Al-Mustapha ya nuna matukar damuwarsa kan rashin tsaro da ake fama da shi a kasar yana mai cewa akwai wasu da ke son tarwatsa kasar

FCT Abuja - Tsohon babban jami'in tsaron marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha a ranar Asabar, ya zubar da hawaye kan batun rashin tsaro a Najeriya.

Ran dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Action Alliance (AA) ya motsa a lokacin da ya tarbi gamayyar kungiyoyin matan kirista na arewa a gidansa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

Al-Mustapha
Al-Mustapha Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Abin da Najeriya ke bukata shine shugabanci. Ya kamata mu fita daga inda muke kuma mutane za su zo su yi amfani da addini su ce 'saboda shi musulmi ne, ba zai iya wannan ba; saboda shi kirista ne, ba zai iya zama wannan ba."

Tsohon babban dogarin ya ce:

"Wadannan sune abubuwan da suka kashe Najeriya a jiya kuma suna amfani da shi don kashe Najeriya gobe. Ba za mu yarda da haka ba. Ga ni zaune kusa da ku; ke yar uwa ta ne. Cikin ku akwai iyaye. Za mu mutu wurin kare ku."

Ya kara da cewa wasu na yaudarar yan Najeriya.

Al-Mustapha ya yi ikirarin cewa wasu mutane da bai bayyana su ba suna kokarin tarwatsa Najeriya, Vanguard ta rahoto.

Ya ce:

"Ana wasa da mu a matsayin kasa. Allah mai girma da daukaka ya bude wa wasun mu ido, tun muna matasa. Shekaru na 19 lokacin da na fara sanin yadda ake mulki a Najeriya."

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Yi Magana Da CNN, Ya Bayyana Tanadin Da Ya Yi Wa Arewacin Najeriya Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Ya kara da cewa:

"Abin da kawai ke gaban su shine su kara tarwatsa mu kuma mutane ba su fahimta ba."

Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya

A wani rahoton, Hamza Al-Mustapha, tsohon hadimin marigayi Janar Sani Abacha ya jadada kudirinsa na zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.

Al-Mustapha, wanda shine dan takarar shugaban jam'iyyar Action Alliance, AA, a zaben 2023 ya ce a shirye ya ke "ya sadaukar da rayuwarsa don Najeriya da walwalar yan Najeriya".

Asali: Legit.ng

Online view pixel