Ban San Adadin Mutanen Da Na Kashe Ba, In Ji Aliyu, Dan Shekara 24 Da Ake Zargi Da Fashi

Ban San Adadin Mutanen Da Na Kashe Ba, In Ji Aliyu, Dan Shekara 24 Da Ake Zargi Da Fashi

  • Rundunar yan sandan Jihar Osun ta ce ta yi nasarar kama wani da ake zargi da fashi da kisar gilla, Adamu Aliyu
  • Aliyu, dan shekara 24 ya amsa cewa shine ya kashe wani mai gidan man fetur a Ikire kuma ya kashe mutane da dama da bai san adadi ba
  • Kakakin yan sanda, Opalola ya ce bayan kama Aliyu, an kuma fadada bincike an kamo wasu wadanda ake zargin da suke aiki tare da shi

Osun - An kama wani mai aikin gini, Adamu Aliyu, tare da wasu mutane hudu kan zargin fashi da makami da kisar gilla inda ya ce ba zai iya tuna adadin mutanen da ya kashe ba, rahoton The Punch.

Yan sanda sun yi holen Aliyu, wanda ke zaune a Ikire, Jihar Osun, da abokinsa, Yusuf Idris da wasu mutane uku a Osogbo kan zarginsu da hada baki da wasu wurin kashe wani manajan gidan man fetur, Fatai Adigun a Aku, garin Ikire.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

Taswirar Jihar Osun
Ban San Iya Adadin Mutanen Da Na Kashe Ba, In Ji Aliyu, Dan Shekara 24 Da Ake Zargi Da Fashi. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dan shekara 24, wanda ya amsa cewa shi ya kashe manajan gidan man, ya ce mahaifin Idris ya bashi kwangilar kashe mutumin, ya kara da cewa wanda an biya N250,000, Vanguard ta rahoto.

Matashin, wanda ya ce iyayensu biyu dukka sun mutu yana karamin, ya ce:

"Ba zan iya kidaya adadin mutanen da na kashe ba. Mun kuma kwace babura da yawa a Ikire. Galibi mu kan siyar da abubuwan da muke sacewa. Ina ganin na kashe fiye da mutum 10.
"Tare da Yusuf Idris na ke aiki. Mahaifinsa ya dauke mu haya mu kashe mutumin. An fada min mace ta bashi aikin. Mun tafi gidan man da safe muka tarar da mutumin. Aboki na, Idris, ya buga masa makami a kai kuma ya mutu."
"Mun sace N100,000 a wurin sannan muka tsere. Bayan sayar da baburan da muka sace, na samu fiye da N1.5m amma na kashe wurin siyan abinci, tufafi da wiwi."

Kara karanta wannan

Na Ga Al'arshin Ubangiji: In Ji Bokan Da Ya Farka Daga Akwatin Gawa Kwana Biyu Bayan Mutuwarsa A Nasarawa

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan Osun, Yemisi Opalola, ya ce bayan samun bayanan sirri a ranar 3 ga watan Satumba, bayan fashi da aka yi a Koteyemu/Aku a Ikire, yan sanda da faran hula suka shiga unguwar suka kamo wanda ake zargin, Adamu Aliyu.

Opalola ya ce an fadada bincike inda aka sake kamo sauran mutum uku da ke aiki tare da babban wanda ake zargin a wuraren da suke boye wa a garin.

Yadda Fasto Ya Saka Ni Na Kashe Mahaifiya Ta Da Adda, Mata Mai Shekara 30

A wani rahoton, rundunar yan sanda na jihar Ondo ta kama wata mata, Blessing Jimoh, mai shekaru 30 saboda kashe mahiyarta, Ijeoma Odo The Nation ta ruwaito.

Blessing ta ce ta halaka mahaifiyarta da adda bayan fasto ya fada mata cewa mahaifiyar mayya ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel