Na Ga Al'arshin Ubangiji: In Ji Bokan Da Ya Farka Daga Akwatin Gawa Kwana Biyu Bayan Mutuwarsa A Nasarawa

Na Ga Al'arshin Ubangiji: In Ji Bokan Da Ya Farka Daga Akwatin Gawa Kwana Biyu Bayan Mutuwarsa A Nasarawa

  • Wani abin mamaki ya faru a garin Gidan Angalu a karamar hukumar Toto ta Jihar Nasarawa yayin da wani boka, Godwin Ugeelu Amadu ya farko bayan mutuwarsa da kwana biyu
  • Amadu, ya farka ne ya kuma fito daga cikin akwatin gawar da aka saka shi a lokacin da ake daf da birne shi a garinsu, hakan yasa mutane suka tarwatse
  • Bayan yan kwanaki, bakinsa ya bude ya kuma bada bayanai dangane da abin da ya gano a wurin da ya ce aljanna da suka hada a abokansa da suka mutu, har da al'arshin Ubangiji ma ya ce ya gano

Nasarawa - Godwin Ugeelu Amadu dan shekara 59 wanda aka sanar da mutuwarsa ya farka ya fito daga akwatin gawar daf da za a birne shi ya bayyana abin da ya gani a aljanna kwana biyu bayan mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Yadda saurayin diyata dan China ya shiga har gida ya caccaka mata wuka, inji mahaifiyar Ummita

The Nation ta rahoto cewa lamarin ya girgiza mutanen garin Gidan Angalu a karamar hukumar Toto na Jihar Nasarawa.

Godwinn Amadu
Bokan Da Ya Farka Daga Akwatin Gawa Daf Da Za A Birne Shi Ya Fada Abin Da Ya Gano A Aljanna. Hoto: @TheNationNews.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke bada labari game da mutuwarsa da tashi daga matacce, Amadu ya ce ba zai iya tuna dukkan abin da ya faru yayin gwagwarmayarsa da mutuwa ba sai dai yana cikin azaba a lokacin, ya ji sauki sannan ya tsinci kansa a wani duniyan.

Amadu ya ce:

"Na gode wa Ubangiji da ya sake bani wata rayuwar bayan dandana mutuwa. Abin ala'jabi ne yadda Allah ya sake bani wata damar rayuwa don in bauta masa in kuma yadda sakonsa.
"Tafiya ta zuwa aljanna mai sauki ne. Na rude kan abin da Ubangiji ya min. Abin da zan iya tunawa shine ya mantuwa ta kama ni lokacin da na ke rashin lafiya, amma daga baya mutane suka taru a kauyen mu don zaman makoki na.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

"Sararin samaniya ta bude kuma na ga wani abu tamkar babban na'urar satelite na gwal a sama. Ba zan iya sanin ko wannan ne Bible ke kira aljanna ba, amma wani mala'ika mai tsawon kafa 75 ya gaishe ni a kofar shiga.
"Mala'ikan na rike da takobi na gwal kuma akwai wani abu a kansa kamar gashi na gwal. Na kuma ga wasu mala'iku biyu a bayansa rike da littafai masu dauke da kalaman ubangiji.
"Mala'ikun uku sun tattauna na kankanin lokaci sannan daga baya suka bari na shiga birnin aljanna.
"Da shiga na birnin, na hadu da wani aboki na tun muna yara shekaru 22 da suka gabata. Sunansa Choko Aguma. Shine ya zagaya da ni birnin da kowa ke bautan Ubangiji.

Amadu ya cigaba da cewa:

"Ya tambaye ni game da wasu mutane amma na fada masa ban san inda wasu suke ba, wasu kuma suna da rai amma wasu sun dade da mutuwa.

Kara karanta wannan

Matar Aure ta Maka Mijinta a Kotun Saboda Baya Cin Abincinta

"Kimanin tsawon yardi 450 na ga wani abu mai kama da al'arshin Ubangiji, wani rubutu da ke cewa "rahama da afuwar Ubangiji' ya dauki hankali na."
"Don haka zan iya tabbatar maka cewa inda na tafi aljanna ne ba wuta ba, kuma na dawo lafiya da kwarin gwiwar yada kalaman ubangiji har karshen rayuwa ta."
"Na bawa Ubangiji rayuwa ta. Tabbas akwai shi.
"Da na ke aljanna, an fada min yadda 'ya'ya na suka yi kokarin ceton rayuwa ta. An kuma fada min abin da na aikata a matsayin boka, duk abin da ya faru kafin mutuwa ta da yadda ake shirin birne ni lokacin da almasihu ya bayyana ya tada ni daga matattu.
"An fada min cewa almasihu ta tada ni ne domin idan aka kai ni kabari aka rufe da kasa zai yi wuya in iya fitowa daga kabarin saboda nauyin kasa.
"Na farko kuma na ji sanyi. Na fito daga akwatin gawar kuma mutanen da suka zo zaman makoki da mata na da yara na suka fara guduwa."

Kara karanta wannan

Kannywood: Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Naje Gidan Gala Har Na Taka Rawa Da Yan Mata, Tahir Fage

Amadu ya kara da cewa:

"Na gode wa Allah saboda ya ji addu'ar 'ya'ya na wadanda ke son ganin na shekaru 86 domin in ga yadda za su zama muhimman mutane a garin mu. Na gode wa Allah, imaninsu yada ubangiji ya dawo da ni."

Jigawa: Yadda Yan Sanda Suka Ceci Wasu Mutane 7 Da Ake Daf Da Birne Su Da Ransu

A wani rahotn, rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Jigawa a hana mutanen gari a karamar hukumar Birniwa birne wasu mutum bakwai da ransu, The Nation ta rahoto.

An gano cewa an yi jayayya tsakanin yan sanda da iyalan mutanen bakwai wanda gini ya rufta musu a kauyen Bursali a karamar hukumar Birniwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel