Yadda Fasto Ya Saka Ni Na Kashe Mahaifiya Ta Da Adda, Mata Mai Shekara 30
- 'Yan sanda a jihar Ondo sun cafke wata mata da ta kashe mahaifiyarta mai suna Ijeoma Odo
- Matar, Blessing Jimoh ta ce wani fasto ne ya fada mata mahaifiyarta mayya ce
- Hakan yasa ta yi amfani da adda ta yanka wuyar mahaifyarta a lokacin suna gona
Rundunar yan sanda na jihar Ondo ta kama wata mata, Blessing Jimoh, mai shekaru 30 saboda kashe mahiyarta, Ijeoma Odo The Nation ta ruwaito.
Blessing ta ce ta halaka mahaifiyarta da adda bayan fasto ya fada mata cewa mahaifiyar mayya ce.
DUBA WANNAN: Nasara Daga Allah: Bidiyon Makaman Da Sojoji Suka Ƙwato Bayan Kashe Ƴan Boko Haram 48 a Borno
An yi holen ta tare da wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.
An ce faston yanzu ya tsere don gudun kada hukuma ta damko shi.
Blessing ta ce tana yara hudu kuma ta aikata laifin ne a lokacin da suke aiki tare a gona a Ile-Iluji.
Ta yi ikirarin cewa hankalinta ya gushe a lokacin da ta aikata laifin.
A cewarta, "Wani abu ne da ke damu na ya saka ni na kashe mahaifiya ta. Ban yi farin cikin abin da na aikata ba.
KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Bindige Tsohon Shugaban PDP Har Lahira a Niger, Sun Sace Matarsa
"Na yanka wutan ta da adda. Fasto ne ya fada min ita mayya ce kuma na tafi in roke ta. Mahaifiya ta yar asalin jihar Enugu ne. Muna ta neman faston amma ba mu gan shi ba."
Kwamishinan yan sanda na jihar Ondo, Bolaji Salami, ya ce za a gurfanar da wacce ake zargin nan bada dadewa ba.
A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.
Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.
Asali: Legit.ng