Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Ghali Na'abba Ya Koma PDP

Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Ghali Na'abba Ya Koma PDP

  • Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Hon Ghali Umar Na'abba, da magoya bayansa sun koma jam'iyyar PDP
  • A wurin taron tsofaffin yan majalisa, Na'abba yace ya yi dana sanin shiga APC, jam'iyyar da ta kawo koma baya a Najeriya
  • Yace zasu yi aiki tukuru wajen sake maida jam'iyyar PDP kan madafun iko domin tun barinta Aso Villa komai ya lalace

Abuja - Tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Honorabul Ghali Na'Abba, ya sauya sheƙa daga APC zuwa jam'iyyar PDP, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Yace jam'iyyar APC mai mulki wacce ya shiga shekaru biyu da suka gabata, Annoba ce kuma masifa ce da ta maida Najeriya baya.

Hon. Ghali Na'Abba.
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Tarayya, Ghali Na'abba Ya Koma PDP Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Na'Abba yace tabbas APC zata girbi abinda ta shuka zata haɗu da fushin 'yan Najeriya idan Allah ya kaimu zaben 2023 saboda jefa ƙasa cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsagin Wike Sun Bazo Wuta, Atiku Ya Kafa Sharuɗdan Tunɓuke Shugaban PDP Na Ƙasa

A wata sanarwa da Dr Golu Timothy, ya fitar, an sanar da sauya shekar Na'Abba ne a wurin taron tsofaffin mambobin majalisar wakilai da ya gudana jiya a Abuja karkashin jagorancin tsohon mataimakin Kakaki, Austin Okpara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace Honorabul Ghali Na'abba tare da ɗumbin magoya bayansa a jihar Kano da sauran jihohin Najeriya sun koma PDP domim ba da gudummuwar ɗora Atiku Abubakar kan madafun iko a shekara mai zuwa.

PDP ta shirya ceto Najeriya - Austin Okpara

Da yake jawabi a wurin taron, Okpara yace jam'iyyar PDP ta shirya koma wa kan madafun iko domin ta ceto tattalin arziƙin ƙasar nan daga rushe wa.

Ya ƙara da cewa shekaru Takwas da PDP ta bar mulki komai ya lalace a ƙasar nan don haka da zaran ta koma kan kujerar mulki, mutane zasu samu salama.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja

A wani labarin kuma Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Yi Kus-Kus da Wani Gwamnan APC

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, na jam'iyyar APC ya ziyarci tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar NNPP yace ya karɓi bakuncin gwamnan ranar Laraba da daddare a Minna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel