Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja

Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja

  • Sanata Kabiru Gaya ya yi rashin 'dansa Barista Sadiq Gaya mazauni birnin tarayya Abuja
  • An yi jana'izar Barista Sadiq Gaya bayan la'asar misalin karfe 4 na yammacin Talata
  • 'Yan uwa, abokan siyasa, har da yan adawa sun aika sakon jajantawa da Sanata Kabiru Gaya

Dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltan mazabar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya yi rashin daya daga cikin 'yayansa.

'Dan masu suna Sadiya Kabiru Gaya, ya rasu ne ranar Talata 13 ga Satumba kuma an yi jana'izarsa da yamma bayan Sallar La'asar a birnin tarayya Abuja.

Marigayin ya kasance Lauya da hukumar manajin dukiyoyi watau AMCON dake Abuja.

Hussaini Ambo Indabwa, Mai magana da yawun mahaifinsa Sanata Kabiru Gaya, ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Matashin Da Ya Mayar Da Kwalin Digirinsa Jami'a Ya Samu Tallafin N500,000

Sadiq ya bar mata guda da 'yaya biyu.

Kabiru Gaya
Allah Ya Yiwa Dan Sanata Kabiru Gaya Rasuwa a FCT Abuja
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin wadanda suka kai gaisuwa akwai Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kai gaisuwar ta'aziyya a gidansa dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel