An Gwabza Yaki Tsakanin Boko Haram, ‘Yan ta’adda Sun Kashe Kansu da Kansu

An Gwabza Yaki Tsakanin Boko Haram, ‘Yan ta’adda Sun Kashe Kansu da Kansu

  • Rigima ta barke a tsakanin ‘yan kungiyar ISWAP da wasu sojojin Abubakar Shekarau a jihar Borno
  • Ana zargin ‘Yan Boko Haram sun gamu da fadan da ya fi karfinsu a lokacin da suka je fashi da makami
  • An rasa sojojin ‘yan ta’addan ne a lokacin da rundunar sojojin Najeriya ke yi masu lugude da jiragen sama

Borno - Wani mummunan fada ya barke tsakanin mutanen Marigayi Abubakar Shekarau da ‘yan bangaren kungiyar ISWAP da ke ta’adi a Afrika ta yamma.

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa rigimar ta kaure ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba 2022, wanda hakan ya jawo aka rasa ‘yan ta’adda da-dama.

Daga cikin wadanda aka kashe a dalilin wannan rigima akwai wani ‘Kundu’, wanda jagoran ‘yan ta’addan ne, haka zalika dai an hallaka wasu sojojin barkatai.

Kara karanta wannan

Ruwan Wuta: Jirgin Yakin Soji Ya Halaka Bashir Iblis da Wasu Ƙasurguman Yan Ta'adda a Arewa

Rikicin ya barke ne a garuruwan Dikwa da Bama, duk a jihar Borno a yankin Arewa maso gabas.

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Kundu da sojojinsa sun je fashi da makami ne sai wasu mayakan kungiyar ISWAP a babura suka yi masu targon rago.

Dakarun na ISWAP sun zo a kan babura shida, kowane babur yana dauke da mayaka uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sojoji
Sojojin Najeriya da ke yakar Boko Haram Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An yi haka - Zagazola Makama

Zagazola Makama wanda masani ne a sha’anin tsaro da rikicin Boko Haram ya tabbatar da aukuwar wannan lamari a shafinsa, yace an kashe mayaka takwas.

A cewar Zagazola Makama, an yi wa ‘yan bangaren Marigayi Shekau illa a harin, yayin da aka samu wadanda suka ji rauni a cikin mayakan kungiyar ISWAP.

Majiyar ta shaida cewa a karshe sojojin Boko Haram sun tsere, sun bar baburan da suke kai. A karshe dai kowane bangare bai ji dadin arangamar da aka yi ba.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro Sun Ceto Jariri ‘Dan Wata 13 Daga Hannun Masu Garkuwa da Mutane

"Mummunan yaki ya kaure tsakanin ‘yan ta’addan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayaka da yawa a bangaren ‘yan ta’ddan Boko Haram
Sannan an yi wa wasu sojojin ISWAP rauni. ‘Yan Boko Haram sun arce da kafafunsu, suka bar baburansu a hannun ‘yan kungiyar ISWAP."

- Zagazola Makama

Garkuwa da mutane

Yayin da ake fama da yawaitar satar mutane, kun ji labari cewa Jami’an ‘yan sanda sun tashi tsaye domin kawo tsaro da zaman lafiya a Najeriya.

A makon nan aka ji labari Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Edo su hallaka ‘yan bindiga a Uhunmwondem sun ceto wani jariri da aka dauke shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel